Da Dumi Dumi

Za yi zaben raba-gardama domin ba Putin damar ci gaba da mulkin Rasha  zuwa 2036

Vladimir Putin
Vladimir Putin

Al’ummar kasar Rasha za su gudanar da zaben raba-gardama kan yiwuwar sake tsayawa takarar Shugaban Kasar, Bladimir Putin, a zaben 2024 da kuma sauya kundin tsarin mulki da tsarin siyasar kasar, a ranar 22 ga Afrilu mai zuwa.

Bayanan da suka fito daga fadar gwamnatin kasar ta Kremlin, sun  ce Shugaba Putin ya yanke hukuncin gudanar da zaben raba-gardama a ranar 22 ga Afrilu kan yiwuwar yin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar.

A kan haka, al’ummar kasar za su bayyana a rumfunan zabe su amsa tambayar “Ko kun amince a yi sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar?”

Idan har fiye da kashi 50 cikin 100 na wadanda suka kada kuri’ar suka amince da haka za a iya sauya kundin tsarin mulkin kasar, inda Putin zai iya ci gaba da mulki bayan zaben 2024.

Idan kuma aka samu amincewar Majalisar Dattawan Kasar, Putin, zai iya tsayawa takara wa’adi na uku, wato zai iya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2024 lamarin da ke nuna cewa zai iya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki har shekarar 2036.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya