✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zabe: Gwamnan Osun ya ayyana Juma’a a matsayin hutu

Gwamnan ya bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar hutun don shirin zaben ranar Asabar.

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan gwamnati domin shirya wa zaben ’yan majalisar dokoki a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Malam Olawale Rasheed, mai magana da yawun gwamnan, ya fitar a ranar Alhamis a Osogbo.

Ya ce an bayar da hutun ne don mazauna jihar su samu damar zuwa rumfunan zabensu domin kada kuri’a a ranar Asabar.

Sanarwar ta shawarce au da su kasance masu zaman lafiya da bin doka da oda yayin da suke shirye-shiryen tunkarar zaben.

“Ina kira ga al’ummar Jihar Osun da su fito su yi amfani da ’yancinsu wajen yin zabe.

“Wannan zaben yana da matukar muhimmanci domin za ku zabi ’yan majalisar da za su yi aiki tare da ni.

“Dole ne ku yi zabe domin ’yancinku ne,” in ji shi.

Ba za a yi zaben gwamna a jihar ba kasancewar zaben gwamna ya gudana a ranar 16 ga Yuli, 2022.