✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zabe na haddasa fitina – Gwamna Yuguda

A cikin watan Agustan da ya gabata ne aka samu ambaliyar ruwa a cikin garin Bauchi da wasu kananan hukumomin Jihar Bauchi, lamarin da ya…

 Malam Isa Yuguda Gwamnan Jihar BauchiA cikin watan Agustan da ya gabata ne aka samu ambaliyar ruwa a cikin garin Bauchi da wasu kananan hukumomin Jihar Bauchi, lamarin da ya haifar da asarar dukiya da rayuka. Bayan zagayawar da Gwamna Isa Yuguda ya yi a cikin garin Bauchi, wakilinmu ya tattauna da shi game da lamarin da kuma wasu batutuwa:

Aminiya:Me za ka ce game da ambaliyar ruwa a wasu sassan garin Bauchi da kewaye?
Gwamna Yuguda: Ina jan hankalin kowa kan yanayin da muke ciki musamman yadda wasu ’yan uwa ke yin gini a magudanun ruwa ko sanya shara a cikin magudanun ruwa ko lambatu. Ina kira ga mutane su daina wannan dabi’a saboda illa ce da ke shafar mutane da dama. Kuma sakamakon ruwan da aka yi rijiyoyi da shadda sun cika, dole ruwa ya hadu da bahaya, idan haka ya faru za a iya samun cututtukan kwalara. Don haka nake kiran mutane su rika tafasa ruwan da za su sha su tace a duk inda ake da shadda kusa da rijiya. Gwamnati za ta bayar da maganin tace ruwa na Chlorine don zubawa a cikin rijiyoyin don kashe kwayoyin cuta saboda kula da lafiyar jama’a. Ina kuma jan hankalin jama’a game da shara ta yau da kullum a unguwanni, a yi kokari kowane mako a fito a yi shara a daina gini ko zuba shara a magudanun ruwa. Duk wanda ya aikata haka a sanar da hukuma za ta dauki mataki a kansa.
Aminiya: Me za ka ce ganin yadda ake ci gaba da samun ruwan gidaje na rushewa?
Gwamna Yuguda: Binciken kimiyya ya nuna wannan ruwa za a ci gaba da yin sa nan da shekaru masu zuwa, badi ma (ana sa ran) za a yi kuma na shekarun gaba zai fi na yanzu. Don haka ya kamata kowa ya zauna da shirin tarbar wannan ruwa mai yawa a shekaru na gaba, kowa ya san da wannan musamman wadanda suke Arewa irin yankin Kirfi masu manyan koguna, kowane mazaunin bakin kogi ya tashi ya koma tudu don kada ruwan ya zo ya yi masa barna da fatar Allah Ya tsare mana dukiyoyinmu da rayuwarmu. Wasu sun yi asarar dukiya wasu sun yi rauni, domin ko ni da kaina na ga yaron da aka ciro shi daga cikin ruwa, kuma  mutane da kansu ya kamata su tashi su gyara magudanun ruwansu, saboda gwamnati ba za ta iya yin komai ba, saboda kudin da yake cikin baitulmali ba ya da yawa. Kuma akwai ayyuka irin su samar da ruwa da tsaro da lafiya da ilimi da tsabtace ruwan sha, kullum sai an zuba sinadarin kulorin na Naira miliyan 20 a madatar ruwa ta Gubi kafin a ba mutane ruwa su sha. Don haka ba za a kwashe kudi a yi  ta tona lambatu kurum ba.
Na shiga cikin GRA da wasu unguwanni na ga abin tausayi saboda yadda mutane suka gina katanga a kan magudanun ruwa, inda ruwan ke zuwa ya rasa mafita ya shiga gidan wasu, idan kuma aka ce mutum ya bude hanyar ruwa a gidansa, sai ya ce ba zai yi ba, don haka nake kiran mutane su tausaya wa juna domin makwabta su kwana lafiya da iyalansu. Kowa ya san akwai hakkin makwabtaka. Na fita da yamma har dare na zaga gari. Don haka yanzu karfe 11:00 na dare na tara ku domin ku sanar da mutane su kare kansu.
Aminiya: Ko akwai shiri da gwamnatinka ta yi na tallafa wa wadanda rushewar gidajen ta shafa musamman tsugunar da su ko taimaka musu?
Gwamna Yuguda: Akwai Kwamishinan Ayyuka na Musamman yana yawo duk fadin jiha don ganin halin da ake ciki a kowane fanni na rayuwa don gyara jiha, tunda muka zo zango na biyu kowace shekara sai na bayar da kudi an sayi baro-baro da diga da cebura da sauran kayan aiki don ba masu unguwanni su gyara magudanun ruwa, kuma idan ba domin ruwa mai yawa da aka yi ba, ba za mu samu wannan matsala ba, domin a bara babu.
Aminiya:A kasashen duniya idan an hango matsala tun wuri ake kwashe mutane kafin ta auka musu, me ya sa ku masu mulki a Najeriya ba ku yin haka?
Gwamna Yuguda: Ka san Najeriya ba mu da kudi yanzu, mutane sun dauka ana zuwa inji ne a yi ta buga kudi a raba wa mutane, gwamnati na da tsari kamar yadda kowa ke fita ya yi aiki a ba shi albashi, haka gwamnati ke fita ta nemi kudi ta zuba cikin aljihunta, wuraren da gwamnati ke samun kudi akwai haraji, ban san harjin nawa kake biya ba a shekara?
Aminiya: Akwai maganganu da ake yi cewa za a nada ka shugaban kungiyar gwamnonin  Najeriya mene ne gaskiyar lamarin?
Gwamna Yuguda:  Abu uku ne suka kafa wannan kungiya, auna aikin juna, ’yan Najeriya su sani kanmu a hade yake da kuma tsarin mulki don inganta tattalin arziki, kowane mako muna zama karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasa muna tattauna batun tattalin arzikin kasa, idan za mu zauna gobe sai mu tattauna yau, kuma muna da kwararru cikinmu idan babu za mu nema a tattauna kafin mu shiga zaman kungiyar gwamnoni ba sai kowa ya tashi ya yi jawabi ba, mutum daya ke tsayawa ya yi magana a madadinmu, ba albashi ake ba mu ba, ba komai ba. To mene ne na wahalar da kai. Amma abin da ke faruwa me zai sa wani ya maida jagorancin kungiyar gwamnoni na ko-a -mutu ko-a-yi rai, dole sai ka zamo shugaba, kowa ya san abin da zabe ke haddasawa, don haka muka guji zabe a cikin kungiyar gwamnoni. A nan mun gani da idonmu yadda ’yan CPC suka yi ta karkashe mutane ’yan bautar kasa da sauransu saboda siyasa. Don haka idan aka ce dole sai an yi zabe a kungiyar gwamnoni dole za a samu fitina, mu kuma ba ma so kungiyar ta rabu. Saboda ko kungiyar gwamnonin Amurka ba a zabe, su ne uwar siyasa daidaitawa ake yi, idan an yarda da mutum dole ya yi abin da ake so. To me ya sa shi wannan zai ce dole sai ya zama shugaba, mu ’yan iska ne? Don haka ba za mu yarda ba.
Aminiya: Akwai wasu alkawurra da ka yi tun bayan hawanka wannan kujera amma har yanzu mutane ba su gani a kasa ba me ya sa?
Gwamna Yuguda: Ga shi kuma an ce saba alkawari babban laifi ne, amma idan kun duba ai mun cika wasu, haka kuma mun kasa samun halin cika wasu saboda rashin kudi ne, ka san ba zan dauki kudin aljihuna na yi ta aiki da shi ba, balle ba ni da shi. Wallahi ajiyata a banki ba ta wuce ka samu Naira milyan biyu ko uku ba, sai ko kadara kurum, na san ina da ita amma ruwan kudi babu, balle kuma gwamnati wacce a kullum ake kukan rashin kudi a cikinta, don haka mutane ya kamata su kara hakuri a kuma gode mana game da dan abin da muka iya gudanarwa.