✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2015: Jonathan shi ya kayar da kansa

A makon jiya ne tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da littafinsa mai suna ‘My Transition Hours” a yayin bikin cikarsa shekara 61 da haihuwa…

A makon jiya ne tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da littafinsa mai suna ‘My Transition Hours” a yayin bikin cikarsa shekara 61 da haihuwa inda ya yi bayanin yadda aka gudanar da zaben shekarar 2015 da kuma dalilan da suka sanya ya fadi a zaben.

A cikin littafin ya yi bayanai masu dama wadanda suka jawo cece-ku-ce saboda bayanan nasa ba sun yi kama da na mutumin da ya shugabanci Najeriya ba, domin ya fito karara yana sukar wani bangare na kasar nan tare da zargin cewa wannan bangaren ne ya yi kutun-kutun da ya kai ga ya rasa mulkin kasar nan.

Hausawa suna cewa idan maye ya manta uwar da ba ta manta ba, idan shi tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya manta al’ummar Arewa ba su manta da irin watsi da al’amarinsu da ya yi a lokacin mulkinsa ba.

A lokacin da Jonathan ya karbi mulki bayan rasuwar marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ya nuna karara ta furucinsa da ayyukansa cewa shi babu ruwansa da ’yan Arewa, domin  a lokacinsa ne matsalar Boko Haram ta gawurta, ana ta kashe mutane kamar kiyashi, amma bai dauki wani mataki mai karfi ba, don a ganinsa an fito da Boko Haram ne domin a muzanta gwamnatinsa, shi ya sanya duk masifar da mutanen Maiduguri suka shiga bai je ya jajanta musu ba, da aka matsa masa da tambaya kan dalilin da ya hana shi zuwa sai ya ce wai saboda an rufe filin jirgin saman Maiduguri ne. Amma da zabe ya karato sai aka gan shi ya sanya kayan soja ya kai ziyara yankin, saboda a wannan lokaci yana bukatar kuri’a.

Duk inda aka kai hari ta hanyar sanya bama-bamai a garurruwan da ke Arewa bai taba kai ziyara ya yi musu jaje ba, amma idan harin da aka kai ya shafi wadansu mutane da yake ganin nasa ne, nan da nan zai kai ziyara wurin. Haka ya yi lokacin da aka sanya bam a wani coci a garin Madalla da ke Jihar Neja, har kuka ya yi a wurin. Haka nan lokacin da bam ya tashi a ofishin buga jaridar  ‘Thisday’ ya kai zai ziyara wurin, haka kuma lokacin da aka tayar da bam a tashar mota ta Nyanyan a Abuja  ya kai ziyara wurin saboda ba ’yan Arewa ne abin ya fi shafa ba, amma sauran wuraren da bama-baman suka yi ta tashi watsi da su Jonathan ya yi.

Sannan kuma a wannan lokaci ne aka mayar da yankin Arewa tamkar fagen yaki, aka sanya wuraren binciken ababen hawa a cikin garurruwa da manyan hanyoyi ana cin zarafin duk wani mutum da aka gan shi ya sanya sutura ta mutunci, babu irin cin kashin  da mutanen Arewa ba su gani ba a wancan lokacin.

A bangaren nade-naden mukamai kuma haka ya mayar da ’yan Arewa saniyar-ware, ya rika cire su daga mukamansu yana maye gurbinsu da ’yan Kudu, abin da ya faru da tsohon Babban Hafsan Sojan Najeriya, Janar Abdurrahman Dambazau da tsohon Gwamnan Bankin Najeriya, Sarkin Kano na yanzu, da tsohon Shugaban Hukumar Shige da Fice sun isa misali.

Haka kuma kiri-kiri a zamaninsa aka mayar da coci wurin fitar da muhimman bayanan da suka  shafi gwamnati, domin Jonathan ya fito da wani salo ne a lokacin,  inda a kowane mako ranar Lahadi yake zuwa coci daban-daban a garin Abuja inda yake yi musu bayanin ya sanar da wani muhimmin mataki da gwamnatinsa za ta dauka. ’Yan Darikar Katolika ne kawai suka nuna masa cewa hakan da yake yi bai dace ba, amma duk da haka bai bari ba, domin shi a ganinsa ’yan Arewa Musulmi ba su kaunarsa, duk da cewa akwai mutane da dama irin su Tanko Yakasai na Kano da Walid Jibril da suka jefa rayukansu cikin hadari saboda Jonathan, amma duk da haka Jonathan bai raga wa ’yan Arewa ba, duk da cewa shugaban jam’iyyarsa ta PDP Ahmad Adamu Mu’azu dan Arewa ne, amma idonsa ya rufe, a gabansu ake cin mutuncin mutanen Arewa.

Bayan ya ci zaben shekarar 2011 ya bayyana wa ’yan kabilar Ibo mazauna yankin Arewa lokacin da suka kai masa ziyara a fadar Shugaban Kasa cewa su ne suka zabe shi a yankin Arewa, ba ’yan Arewa ne suka zabe shi ba.

A lokacin da aka sace ’yan matan makarantar Chibok a Jihar Borno cewa ya yi karya ce, har matarsa Patience Jonathan ta kira shugabar makarantar ta ci mata mutunci a fadar gwamnati, inda har ta fashe da kuka tana cewa “ There is God woo,” wai ita a dole an ci mutunci mijinta ta hanyar shirya makircin da za a zubar da mutuncin mijinta a idon duniya, sai da aka dauki lokaci kafin gwamnatinsa ta yarda an sace ’yan matan Chibok, duk da haka ba a dauki kwakkwaran matakin ceto su ba.

Haka dai ya rika nuna wa ’yan Arewa wariya da cin fuska har lokacin zaben shekarar 2015, inda ’yan Arewa suka tashi tsaye suka jajirce domin ganin sun fitar da shi daga Fadar Gwamnatin Tarayya sun koma da shi gida a garinsu Oturke.

A zamanin mulkin Jonathan bayyanannen abu ne cewa ya nuna karara cewa mutanen kasar nan ba daya suke a wurinsa ba, akwai ’yan mowa da ’yan bora. ’Yan yankin Neja Delta kuwa ai a lokacin Jonathan sun san dansu yana mulki, domin kuwa sai fantamawa kawai suke yi, “namu ya samu, lokacinmu ne.”

Domin haka kada Jonathan ya yi kuka da kowa, irin salon shugabancinsa na nuna bambanci ta hanyar fifita wata al’umma fiye wata ne ya jawo masa faduwa a zaben shekarar 2015, domin ’yan Arewa ba mahaukata ba ne da za a ci mutuncinsu su tsaya suna kallo, alhali Allah Ya ba su damar da za su samar wa kansu sa’ida.

Wannan darasi ne ga duk wani mai son shugabancin kasar nan da ya tabbatar ya yi wa kowa adalci idan ba haka ba  ba zai dade ba zai fado, domin zalunci ba ya dorewa. Kuma wadanda suka manta ya kamata su tuna cewa ’yan Arewa ba kanwar lasa ba ne, duk wanda ya ce zai yi babu su, to sai dai ya ga ana yi, domin a tsarin mulkin dimokuradiyya yawan mutane yana tasiri kwarai, kuma Allah Ya hore wa Arewa mutane.