✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2019: Atiku ya daukaka kara a kotun koli

Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP a zaben ranar 23 ga Fabrairu 2019 Atiku Abubakar ya daukaka kara a kotun koli domin kalubalantar hukuncin…

Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP a zaben ranar 23 ga Fabrairu 2019 Atiku Abubakar ya daukaka kara a kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke, inda ta tabbatar da nasarar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP sun jajirce cewa kotun sauraron kararrakin zaben ta yi kuskure wajen amincewa da cancantar Buhari a matsayin zabbaben shugaban Najeriya, kamar yadda daya daga cikin lauyoyin PDP Mike Ozekhome (SAN) ya sanarwa manema labarai.