Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Zaben 2019: Dan takarar Gwamnan APC na Nasarawa ya yaba wa mutanen jihar

Dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Sule ya yaba wa al’ummar jihar musamman magoya bayan jam’iyyar dangane da hangen nesa da suka nuna  waje zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura a matsayin Sanata.

Alhaji Abdullahi Sule ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a gidansa da ke Gudi a Karamar Hukumar Akwanga a jihar jim kadan bayan Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zabe.

ADVERTISEMENT

Ya ce ba shakka al’ummar jihar sun yi zabi nagari idan aka yi la’akari da ayyukan ci gaba da wadanda aka zaba suka gudanar a jihar da kasa baki daya. Sannan ya bukace su da su zabe shi a matsayin Gwamnan jihar da sauran ’yan takarar APC a zaben mai zuwa don ya samu damar aiki da Shugaba Buhari da Sanata Al-Makura domin samar da romon dimokuradiyya a jihar.

Ya bayyana zaben a matsayin mafi ingancin zab da aka gudanar cikin gaskiya da kwanciyar hankali da ba a taba gudanar da irinsa ba a jihar, sannan ya bukaci al’ummar jihar baki daya su dore a haka.

ADVERTISEMENT

A zaben da aka gudanar a jihar, Shugaba Buhari ne ya doke Atiku, sannan a zaben Sanatan Nasarawa ta Gabas, Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na APC ne ya lashe da kuri’a dubu 113 da 156 yayin da abokin karawarsa na PDP Sanata Suleiman Adokwe ya samu kuri’a dubu 104 da 595. A Yammacin jihar kuma Sanata Abdullahi Adamu na APC ne ya yi nasara da kuri’a dubu 115 da 298 inda ya doke Alhaji Bala Ahmed na Jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’a dubu 83 da 615.

Wannan ne karo na farko da Shugaba Buhari ya lashe zabe a jihar tunda ya fara takarar Shugaban Kasa.