✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2019: Kira ga ’yan Najeriya don zabar cancanta

Assalam Editan, fatan alheri a gare ku jaridar AMINIYA mai farin jini. Edita ka ba ni dama in yi kira ga al’ummar Najeriya kan karatowar…

Assalam Editan, fatan alheri a gare ku jaridar AMINIYA mai farin jini. Edita ka ba ni dama in yi kira ga al’ummar Najeriya kan karatowar babban zaben kasa. Yana da kyau mu zabi cancanta, mu sani kuri’arka ’yancinka ce, ka sani kana da hakki ka fito filin zabe ka zabi mutumin da ka san zai kare mutuncinka da addininka, mu kuma dage da addu’a a kan Allah Ya zaba mana mafi alheri. Allah kuma Ya hada mu da shugabanni masu tausayinmu da kishinmu, wadanda za su fifita bukatunmu fiye da bukatun kansu. Yana da kyau talakawa mu daina siyasar kudi, domin kudi mai karewa ne, mu zamo masu kishin kanmu da addininmu, tare kuma da sanin darajar kanmu. Idan muka kasance masu sanin darajar kanmu, su kansu ’yan siyasar kasarmu ba za su rika mai damu ba a bakin komai ba.

Ya Allah Ka taimaki kasarmu Najeriya.

Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki Kano, 07068295953.