✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2019: Mun gaji da tura mota tana bade mu da kura – Hausawan Abekuta

Al’ummar Arewa mazauna Abekuta a Jihar Ogun sun bayyana rashin jin dadinsu bisa irin shakulatin bangaro da halin ko-in-kula da ’yan sisayar yankin ke yi…

Al’ummar Arewa mazauna Abekuta a Jihar Ogun sun bayyana rashin jin dadinsu bisa irin shakulatin bangaro da halin ko-in-kula da ’yan sisayar yankin ke yi masu ta yadda sai idan lokacin zabe ya karaso ne kadai ’yan siyasar ke nemansu, suna zawarcin kuri’arsu.

A cewar Sarkin Hausawan Abekuta, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan lokaci ya yi da ’yan Arewa mazauna Kurmi zasu yi karatun ta-nutsu su zabi wanda zai kula da martabarsu, wanda ’ya’yansu da jikokinsu zasu amfana a tsarin mulkinsa, “a baya sai idan irin wannan lokaci na siyasa ya karato ne zaka ga ’yan siyasa suna kawo mana ziyara babu abin da suke amfanarmu da shi sai dai kawai su dauki dan kudi su bayar a raba, daga wannan lokaci ba zaka sake jin duriyarsu ba sai in kakar zabe ta matso, babu wani alfanu da jama’ar mu ke samu ta fuskar cigaba na romon dimokoradiyya. Don haka a yanzu kan mage ya waye kuri’ar al’ummarmu ta wanda zai kawo mana cigaba ne, wanda zai kawo mana abubuwan cigaba a unguwanninmu, ’ya’yanmu da jikokinmu su amfana,” inji shi.

Sarkin Hausawan ya bayyana haka ne a lokacin da daya daga cikin ’yan takarar Gwamna a Jihar Ogun, Shegun Adebgami ya ziyarce su a ranar Juma’ar da ta gabata.

Shegun Adegbami wanda tsohon shahararren dan kwallan kafar Najeriya ne, ya bayyana ziyarar da ya kaiwa Sarkin Hausawan a matsayin ziyarar bangirma kawai ba ziyara mai alaka da manufarsa ta siyasa ba, “ni a Jihar Filato aka haife ni, a cikin ’yan Arewa na taso, wannan ne ya bani damar hulda da ’yan’uwana ’yan Arewa, domin ina fahimtar harshen hausa kwarai da gaske, haka ne ya sanya na ga dacewar na zo mu sada zumunci da ’yan’uwana hausawan wannan yanki,” inji shi.

Ya ce jam’iyyar da yake takarar gwamna a inuwarta, wato jam’iyyar Zineth ta baiwa ’yan Arewa mazauna garin Sabo Abekuata damar bada dansu domin ya tsaya takarar dan majalisar jihar, “wannan shi ne salonmu, yin aiki tare da kowa ba tare da nuna bambanci ba, idan aka kafa gwamnati da danku a ciki a matsayinsa na dan majalisar jiha shine zai kawo maku cigaba a yankinku, duk abubuwan gina al’umma da shi za a tsara, kun ga wajibinsa ne ya tuna da ku,” inji shi.

Ya kara da cewa abin takaici ne duba da irin ci bayan da unguwar Hausawa ta Sabo Abekuta ke fuskanta ta fuskar abubuwan more rayuwa, ya ce ya yi mamakin rashin kyaun hanyoyin unguwar da kuma kalubalen da al’ummar yankin ke fuskanta na ruwa da sauran abubuwan more rayuwa.

A martanin da zarkin Hausawan Abekuta Alhaji Ibrahim Hassan Hassan ya bayyana Shegun Adebgami a matsayin dan kasa nagari wanda ya bada gudumawarsa ta fusakar kwallan kafa a shekarun baya, “ni kaina mun yi wasannin kwallo na samun horo tare da shi, da sauran ’yan wasan kwallon kafa irin su Dabid Adele da Kadiri Ikana da Toyin Ayinla da dai sauransu. To yanzu lokaci ya yi da za a dama da hausawa a siyasar Jihar Ogun, domin mun gaji da tura mota tana bade mu da kura.”

Taron wanda ya gudana a fadar Sarkin Hausawan ya sami halartar dattawan ’yan Arewa mazauna Abekuata da shugabannin matasa da manyan limaman garin wadanda suka yi wa kasa addu’ar zaman lafiya duba da karatowar zaben 2019.