✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2019: Ya kamata mu dage da addu’a – Sheikh Bala Lau

Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, a zantawa da ya yi da ’yan jarida a…

Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, a zantawa da ya yi da ’yan jarida a Kaduna kan zabe mai zuwa ya bukaci jama’a su yi ta addu’ar yin sa cikin kwanciyar hankali da sauran batutuwa:

 

Wane kira malam zai yi ga ’yan Najeriya kan zaben da ke tafe?

Babban abin da ya kamata al’ummar Musulmi su a zukatansu shi ne addu’o’in Allah Ya sa a yi zaben nan lafiya a gama lafiya Ya kuma zaba mana shugabanni na kwarai a dukan matakai. Kuma babban kira da nake yi shi ne duk gwagwarmayar da ake yi Allah Ya riga Ya kaddara Ya kuma san wane ne zai shugabanci al’umma. Saboda haka mu dauki abin cikin sauki sannan a yi yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali.

Mu kuma san irin kalaman da za mu rika yi. Alkur’ani ya gaya mana ku fada wa mutane magana mai kyau. Magana mai kyau idan kana fadinta wanda ba ya sonka ma sai ya kaunace ka. Sayyidina Ali (RA) yana cewa wanda duk kalmansa suka zama masu laushi wajibi ne ka ga soyayyar mutane ta koma gare shi. Duk mutumin da yake hakuri da wautar da ake masa a zage shi ko a ci mutuncinsa bai ramawa sai Allah Ya yawaita masa rundunar da za su rama masa.

Wani ya samu Sayyidina Abubakar (RA) a zamanin Manzon Allah (saw) yana ta zaginsa Sayyidina Abubakar bai amsa ba ya sake zaginsa bai amsa ba, can sai ya budi baki ya ce me na yi maka kake ta zagina. Yana fadin haka Manzon Allah (SAW) na wajen sai ya tashi ya bar wajen. Sayyidina Abubakar (RA) ya bi shi ya ce ya Rasulullahi ya zagen ban ce komai ba, kawai na ce me na yi masa sai ka tashi? Sai Annabi (SAW) ya ce ai lokacin da yake zaginka Allah Ya turo mala’ika yana rama maka amma da ka ce mai na yi sai mala’ika ya tafi shi kuma shaidan sai ya zo wajen domin ya zuga ka ku yi fada. Ni ko ba na zama inda ake fada.

Saboda haka dole ne masu siyasa su san irin kalaman da za su yi na zaman lafiya. Da za a dauki hanyoyin magabata na zamantakewa da an samu zaman lafiya. Da an samu cikakken hadin kan al’umma.

Sannan masu bibiyar kafafen sadarwa na soshiyal midiya ina kira gare su su ji tsoron Allah irin yadda ake yada duk labari da ya zo maka ba ka bincika ba ka yada shi na cin mutunci da maganganu wannan ba zai taimake mu ba. Kur’ani ya tabbatar mana da cewa Allah Ya sanya akwai mala’iku da ke rubuta duk abin da muke aikatawa.  Kuma za a tsayar da kai ranar Alkiyama a tambaye ka abin da ka fadi a kan wani. In karya ce, ka ga kuma lokacin tuba ba ta da amfani a cikin ayyukanka na ibada za a dauka a biya shi.

Don haka ina kira ga ’yan jarida su ci gaba da watsa alheri da abin da zai tabbatar da zaman lafiya. Abin da zai taimaki kasarmu shi ne abin da za mu rika yadawa. Shi ya sa Manzon Allah (SAW) ya ce duk mutumin da ya yi imani da Allah da  Ranar Lahira idan zai yi magana ya fadi alheri ko ya yi shiru.

Allah Ya zaba mana shugabanni na kwarai, ba lokaci ne da ya kamata a yi amfani da duniya ba lokaci ne da ya kamata a zabi masu amana da adalci kuma masu tsoron Allah. Idan aka ba ka duniya ka karba ka yi zabe, kila abin da aka ba ka in ya dade maka wata biyu idan an ba ka da yawa ke nan. Bayan nan kuma za ka yi zaman wahala na shekara hudu. Ashe ke nan duk wanda ya ba ka kudi don ka zabe shi ka lura yana son ya sayi kuri’arka ce, amma wanda bai ba ka ba kuma ka ga ya cancanta kawai ka zabe shi.

Dama shi shugabanci tsare addini ne da tsare mutuncinka da jininka da kwakwalwarka da zama lafiya. Idan ka samu wanda zai yi maka wannan, ko bai ba ka komai ba, ka zabe shi domin Hausawa sun ce zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Hatta masu saurata ma a yanzu sun ce sun gano zaman lafiya ya fi sarki domin in babu zaman lafiya ina za a yi sarauta?

Wane kira za ka yi ga ’yan siyasa kan su mara wa duk wanda ya samu nasara baya domin ci gaban kasa?

Su ’yan siyasa ina kira gare su da su san cewa zaman lafiyar kasar nan ya fi komai domin dama ka shiga zabe ne kodai ka ci ko ka rasa. Idan ka samu sai ka gode wa Allah da wanda ya zabe ka da wanda bai zabe ka ba duk sai ka dauke su a matsayin naka ne kuma ka yi musu adalci. Idan Allah Ya kaddara ba ka samu ba, ta yiwu gaba ka samu saboda haka kada ka ta da hankalinka. Sau da yawa za ka nemi abu kamar ka mutu, a ba ka ya zamanto maka masifa. Akwai wadanda suka nemi mulki ya zame musu masifa har suka mutu, akwai kuma wadanda suka nemi mulki har suka sauka ak an mulki babu kwanciyar hankali. Ashe ke nan ka ga mulkin ya zame musu ba alheri ba.

Akwai wanda kuma bai nema ba sai Allah Ya ba shi kuma ya zama masa alheri. Babu kasar da za ta iya saukar ’yan gudun hijirar Najeriya Allah Ya sauwake. Saboda haka sai mu yi hakuri mu yi wa kasarmu addu’a Allah Ya yi mana zabi domin kasar ta zauna lafiya.

Kana da wani sako ga hukumar zabe?

Hukumar zabe ina kira gare ta ta yi adalci domin da adalci ake cin nasara. Duk mutumin da yake an ba shi cewa shi ne zai sanar da wani ya ci ko wani ya fadi to idan har za a ba shi duniya ya karba don ya ciyar da wanda bai ci ba, to ya ji tsoron tsayuwarsa a gaban Allah. Idan ya tsaya gaban Allah, Allah zai kama shi saboda ya yi zalunci. Saboda Haka hukumar zabe su yi adalci wanda ya ci zabe a ba shi. Wanda bai ci zabe ba ya yi hakuri saboda dole mutum daya ne zai yi nasara.

Su ma jami’an tsaro su ji tsoron Allah kada a yi amfani da su wajen tarwatsa mutane don kada a yi zabe. Masu zabe kuma su fito cikin kwanciyar hankali da tsakanaki ba tashin hankali wajen kada kuri’a.