✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben aure: Yadda wasan yara ya fito da sunan garin Giyade a duniya

Labarin zaben fid-da-gwani kan neman aure na wasan yara da aka yi a garin Giyade da ke Karamar Hukumar Giyade a Jihar Bauchi ya dada…

Labarin zaben fid-da-gwani kan neman aure na wasan yara da aka yi a garin Giyade da ke Karamar Hukumar Giyade a Jihar Bauchi ya dada fito da sunan garin sakamakon yada batun da aka yi ta kafofin sada zumunta  ana nuna da gaske ne.

Bincike da Aminiya ta yi a garin Giyade ya nuna cewa yarinyar da ake batun a kanta, ba ta ma san me ake yi ba.

Shugaban Kwamitin Zaben, mai suna Umar Saleh ya ce, “Abin ya fara ne kamar musu a tsakanin abokai biyu wadanda dukkansu na ikirarin suna son wata budurwa mai suna Hajara, sai suka yanke shawarar gudanar da zaben raba-gardama ko zaben fid-da-gwani.” Saleh ya ce wanda aka kayar sunansa Ibrahim da ma yana da shagon da yake sayar da ruwa a leda wanda nan ne ya kasance wajen haduwarsu. Ya ce lokacin da musayyar ta kawo a yi zabe sai aka ce kowanne daga cikinsu zai gayyato magoya bayansa kuma aka amince a bi dukkan matakan shirya zabe domin a raba gardama.

Saleh ya ce “Sai muka zauna da dukkan bangarorin biyu muka tsara jadawalin gudanar da zabe da rana da lokaci muka kuma kafa kotun sauraron kararrakin zabe, kuma dukkan bangarorin suka amince da tsarin da aka yi muka gayyato ’yan banga da kuma masu tsaro na farin kaya wato Sibil Difens. Bayan an kammala dukkan tsare-tsare an kuma yi zabe, mutum 542 suka kada kuri’a, Yunusa ya samu kuri’a 331 shi kuma Ibrahim ya samu kuri’a 211,” inji shi.

A yanzu kotun suraron kararrakin zabe ne ke jira ta karbi korafi daga wanda aka kayar a zaben don mako guda ne kawai aka dibar masa ya gabatar da korafinsa in kuma ya kasa yin haka to zabe ya zauna.

Wanda aka doke, Ibrahim Adamu mai shekara 22 ya shaida wa Aminiya cewa, shi bai amince da kayen da ya sha ba, don haka zai shigar da kara.  Ibrahim ya ce abin da ya faru ba zai shafi dangantakarsa da abokinsa ba wanda ya kayar da shi ba.

Ya ce dalilin da ya sa zai yi kara shi ne an yi zaben ne a bayan gidan wanda suka yi takara da shi kuma ba yadda za a yi a ce makwabtansa ba su zabe shi ba.

“Ban ji dadin kayen da na sha ba, saboda bai kamata in yi takara a garinmu kuma a kada ni cikin mutanena ba. Saboda haka zan kalubalanci sakamakon kuma in kotun ba ta mini adalci ba zan daukaka kara zuwa wajen hakimi shi kuma duk hukuncin da ya yanke zan bi,” inji shi

A bayanin Yunusa Hamza mai shekara 18 wanda shi ne ya yi nasara a zaben ya ce ya fara son budurwar ce wata uku da suka wuce, lokacin da take zuwa ta sayi ruwan leda a masana’antar ruwan leda da yake aiki na Walima Table Water, yayin da shi kuma abokin takararsa ke sayar da ruwa a shagonsa da ke kan hanyar Kano zuwa Kari, inda abokan ke taruwa.

Ya ce, “Wannan zaben ya bude min ido don in tsaya takarar mukamin siyasa, saboda goyon baya da nake da shi. Tunda na shiga lungu da sako yakin neman zabe, na samu kwarin gwiwar tsayawa takara a kowane lokaci, kuma Allah zai ba ni nasara.”

Yarinyar da ake takara a kanta mai suna Hajara Abdullahi mai shekara 14 wacce take karamar sakandare aji uku ta shaida wa aminiya cewa “Na samu labarin zaben ne ranar Alhamis bayan na dawo daga makaranta, inda na ji wai ana zabe tsakani samari biyu da suke sona. Na dauki abin wasa ne sai ya zama gaskiya.” Hajara ta ce, “Abin da na sani shi ne nakan je in sayi ruwa, watarana na ji daya daga cikinsu yana fada wa abokinsa cewa yana sona saboda halayena na kirki da nagarta da nake da su, sai dayan ya ce yaya za ka ce kana son budurwar da nake mutuwar so. Ni dai nan na bar su na tafi gida. Na yi mamaki kwarai da na ji sun maida abin zabe.”

Ta ce ba ta sa wani ya yi zabe don neman amincewar soyayyarta ba, “Ina musu fatar alheri duk wanda Allah Ya sa zai zama mijina zai zama, na bar komai a hannun Allah, ina tare da iyayena ina musu biyayya duk abin da suka ce shi zan bi,” inji ta

Mahaifiyar budurwar mai suna Hussaina Umar ta ce batun wannan zabe wasa ne don su ba su san komai a kai ba, kuma yin haka ba al’adar mutanen Giyade ba ne, “Mun ji dadi da ba a samu tashin hankali ba.”

Yayan yaron da ya sha kaye Abdulahi Muhammad ya ce su ma iyayensu da danginsu ba su da masaniya kan zaben.

Dan uwan wanda ya yi nasara Adamu Haruna ya ce sun dauki lamarin wasan yara kuma aure ba abin wasa ba ne.

Sakataren Kwamitin Zaben Ibrahim Taldo Giyade ya shaida wa Aminiya cewa wanda aka kayar ya ki amincewa da sakamakon zaben kuma an kafa kwamiti mutun shida da zai saurari korafin, yanzu dai ana jiransa ya gabatar da korafi.

Wani dattijo a Giade mai suna Umar Hussaini ya shaidawa Aminiya cewa abokai ne maza suka yi zaben amma ya bazu a duniya, wanda yau ya zama babban lamari a Giade.