✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben bana: Gargadi ga masu kada kuri’a

Salam Edita, barka da aiki. Zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga dukan ’yan Najeriya masu zabe a zaben da ke tafe a…

Salam Edita, barka da aiki. Zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga dukan ’yan Najeriya masu zabe a zaben da ke tafe a watan gobe, cewa ya kamata mu sa kafa mu yi fatali da duk wanda zai rude mu da ’yan kudade domin samun kuri’unmu. Mu tsaya mu yi binciken kwakwaf wajen zakulo mutanen kirki a kowace jam’iyyar siyasa suke, wadanda za su ciyar da yankunanmu da jihohinmu da ma kasarmu gaba, wadanda idon  muka zabe su, ba za mu yi da na sani ba.

Duk da kiraye-kirayen da al’umma suke yi a kafafe daban-daban hadi da wasu kungiyoyi, wajen zaben mutumin kirki, amma wadansu sukan mance haka lokacin da suka je rumfunan zabe, saboda wadansu bara-gurbin ’yan siyasa sukan yi amfani da wannan dama wajen sayen kuri’a musamman daga mata da mazan da talauci yake addaba. Da fatan Allah Ya sa a yi wannan zabe lafiya a kammala lafiya, muna rokon Allah ya zaba mana shugabanni nagari masu kishin kasa da son ci gabanta.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020.