✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben fid-da-gwani: Rudani ya dabaibaye APC da PDP

A yau Juma’a Jam’iyya mai mulki wato APC za ta fara gudanar da zaben fid-da-gwani, inda za ta fara da zaben wanda zai tsaya mata…

A yau Juma’a Jam’iyya mai mulki wato APC za ta fara gudanar da zaben fid-da-gwani, inda za ta fara da zaben wanda zai tsaya mata takarar Shugaban kasa.

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP kuma za ta fara nata zaben fid-da-gwanin ne a jibi Lahadi, 30 ta hanyar zaben ’yan takarar majalisun dokoki na jihohi.

To sai dai wata guguwa mai karfi da ke barazana ga jam’iyyun biyu tana ta kadawa a daidai lokacin da suke kokarin fara wadannan zabubbuka da za su dora su a kan hanyar fuskantar babban zaben da za a gudanar a badi.

Masu fashin baki kan al’amuran siyasa suna ganin idan Jam’iyyar APC da Jam’iyyar PDP ba su daidaita al’amuransu wajen fito da ’yan takararsu bisa tsari na adalci, ko kuma shugabannin jam’iyyun biyu suka bi son ransu, ko kuma suka goyi bayan wadansu ’yan takarar da jama’a ba sa so, to suna iya fuskantar kalubale sosai a lokacin zabe mai zuwa.

Yadda hidimar take a APC

Jam’iyyar APC ta fuskanci cece-ku-ce mai tsanani a ’yan watannin nan dangane da tsarin da za ta bi wajen fid-da-gwanayenta da za su shiga a fafata da su a zabubbukan da za a gudanar a badi.

Daga farko Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na kasa (NEC) ya amince a yi amfani da zaben ’Yar Tinke wajan fid da ’yan takara. Wannan tsari zai bai wa duk dan jam’iyyar wanda ke da rajista damar kada kuri’a ga wanda yake so a lokacin fitar da ’yan takarar Shugaban kasa da gwamnoni da ’yan Majalisar Dokoki ta kasa (sanatoci da wakilai) da kuma ’yan majalisar dokoki na jihohi.

To amma kuma yawancin gwamnonin Jam’iyyar APC sun nuna rashin gamsuwa da wannan tsari, inda suka nuna sun fi amincewa a yi amfani da tsari zaben sirri kuma na wakilan jam’iyya kadai ta yadda wakilan da aka zakulo daga mazabu ne za su zabi ’yan takara baki daya.

Su dai gwamnoni suna ganin idan aka bi wannan tsari, za su iya samun damar bayar da tikitin tsayawa takara ga mutanen da suke so.

Su kuma wadansu manyan ’ya’yan jam’iyyar kamar sanatoci masu ci da kuma ba sa jituwa da gwawnoninsu, ba sa so ay i amfani da wannan tsari.

Kwatsam ana cikin wannan rudani ne sai Jam’iyyar APC ta fitar ta sabuwar sanarwa a ranar Talatar da ta gabata, inda ta canja tsarin gaba daya, ta yadda wasu jihohin da a da suka ce za su yi amfani da wakilan jam’iyya aka canja musu tsari aka ce lallai kowane dan jam’iyya mai kati yana da damar da zai kada kuri’a wajen fitar da ’yan takarar.

Wani bayani da Kakkin Jam’iyyar na kasa, Yekini Nabena ya fitar, ya nuna cewa yanzu jihohin da aka amince su yi zaben fid-da-gwani ta hanyar ’Yar Tinke tsaye su goma 18 ne da Babban Birnin Tarayya (FCT). Jihohin sun hada da Abiya da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Bayelsa da Kuros Riba da Edo da Ekiti da Imo da Kano da Legas da Neja da Ogun da Ondo da Osun da Taraba da kuma Zamfara.

Yekini Nabena ya ce jihohin da za su yi amfani da wakilan jam’iyya wajen fitar da ’yan takarar su 19 sun hada da Adamawa da Benuwai da Borno da Delta da Ebonyi da Enugu da Gombe da Jigawa da kuma Kaduna.

Sauran su ne Katsina da Kebbi da Kogi da Kwara da Nasarawa da Oyo da Filato da Ribas da kuma Sakkwato.

Binciken Aminiya ya gano cewa wannan sabon tsari jihohin da aka watsa musu kasa a garinsu ta hanyar umartarsu da su yi zaben ’Yar Tinke ba kamar yadda suka shirya a da ba, da suka hada da Bauchi da Kuros Riba da Edo da Imo da Ondo da Ogun da Taraba, hakan yana da alaka ne da rashin daidaituwa a jihohin.

A Jihar Bauchi dai Gwamna Mohammed Abubakar da magoya bayansa ba su ji dadin wannan canji ba, domin tsarin kusan ya share hawayen wadansu ’yan takara ne kamar su Dokta Ibrahim Yakubu Lame da Kyaftin Bala Jibrin da suke kokarin kwace kujera daga hannun Gwamna Abubakar.

Magoya bayan Gwamnan suna ganin idan aka yi amfani da wakilan jam’iyya za su iya samun nasara a wajen fitar da ’yan takarar.

A wata zantawa da wakilinmu wani dan takarar Sanata a Bauchi ta Kudu, Barista Ibrahim Zailani ya bayyana cewa dama su sun kai korafinsu a hedkwatar Jam’iyyar APC a Abuja ne inda suke neman a canja tsarin ta yadda duk wani dan jam’iyya mai kati zai iya jefa kuri’a.

A Jihar Imo ma za a iya cewa Gwamna Rochas Okorocha ya sha kasa domin ya so a bar shi ya yi amfani da wakilan jam’iyya ne wajen fitar da ’yan takara.

Sai dai kuma Mataimakin Gwamna Yarima Eze Madumere da Sanata Hope Uzodinma da Toe Ekechi da Hillary Eke masu adawa da Okorocha suna murna ne ganin cewa za a yi amfani da’Yar Tinke ne wajen zaben fitar da ’yan takara, wanda hakan na iya hana Gwamna Okorocha yin rawar gaban hantsi.

Suna ganin wannan dama ce da za su yi amfani da ita wajen kada surukin Okorocha wato Uche Nwosu a zaben fid-da-gwani.

A Zamfara ma akwai rikici a kasa inda Gwamna Abdul’aziz Yari ya so a bar shi ya yi amfani da wakilan jam’iyya wajen fitar da ’yan takararsa na Gwamna da sauran kujeru. Tuni dai ya fitar da Kwamishinansa na Kudi Alhaji Mukhtar Shehu Idris a matsayin dan takarar Gwamna.

’Yan takarar Gwamna su takwas sun yi bore ga Gwamna Yari kuma sun yi tofin Allah tsine kan matakin da ya dauka wajen fitar da magajinsa.

’Yan takarar da suka hada da Mataimakin Gwamna Ibrahim Wakala da tsohon Gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi an ce sun yi murna da umarnin da jam’iyyar ta bayar na cewa a yi zaben ’Yar Tinke wajen fitar da ‘’yan takarar.

Sauran ’yan takarar da suka yi murna da wannan mataki sun hada da  Sanata Kabiru Marafa da  Ministan Tsaro Mansur dan-Ali da Alhaji Aminu Sani Jaji da Injiniya Abu Magaji da Alhaji Dauda Lawal da kuma Alhaji Mohammed Sagir Hamidu.

Sai dai ana ganin wannan tsari na ’Yar Tinke ma zai bar baya da kura, domin bayan kudade masu dimbin yawa da za a kashe wajen gudanar da shi da kuma ‘tukuicin’ da za a raba wa duk wanda ya shiga layi aka kirga shi, jam’iyyar za ta kasance a kotu domin wadansu da ba za su gamsu da tsarin ba za su je a bi musu hakki.

A wasu jihohi kuma ’yan adawa da ke cikin jam’iyya mai mulkin ba su samu cimma burinsu ba.

Misali a Jihar Kaduna inda irin su Sanata Shehu Sani suke so a yi zaben ’Yar Tinke amma ba su samu nasara ba, wanda hakan ya nuna cewa Gwamna Nasir El-Rufa’i zai ci karensa babu babbbaka ke nan.

Haka kuma akwai gwamnoni masu shirin sake tsaywa takara da kuma za su sheke ayarsu domin ba su da abokan hamayya. Wadannan gwamnoni sun hada da Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da Simon Lalong na Filato da kuma Sani Bello na Jihar Neja.

To sai dai duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi kadai ne dan takarar Jam’iyyar APC a wannan karo, rudani ya dabaibaye shirye-shiryen gudanar da zaben da za ayi a yau Juma’a.

Dalili shi ne jam’iyyar ta ce za ta yi amfani ne da zaben ’Yar Tinke a rumfunan jefa kuri’a sama da dubu tara.

Wannan tsari ya sanya ’ya’yan jam’iyyar cikin tunanin yaya za a gudanar da zaben.

A shekaranjiya Laraba Shugaban Jam’iyyar, Adams Oshiomhole ya rarraba kundin mambobin jam’iyyar ga shugabanninta na jihohi, inda ya ja musu kunne cewa za a kore su idan suka yi amfani da damar da suka samu wajen ba da fifiko ga wadansu ’yan takara.

Fargaba a PDP

Babban hidimar da ke gaban Jam’iyyar PDP dai ita ce kokarin fitar da mutum daya tilo da zai yi mata takarar Shugaban kasa daga cikin mutum 12 da suka nuna sha’awar tsaya mata takara.

’Yan takarar dai sun hada da Alhaji Atiku Abubakar da Sanata Ahmed Makarfi da Alhaji Attahiru Bafarawa da Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo da Sanata Jonah Jang da Sanata Rabi’u Kwankwaso da Alhaji Sule Lamido da Dokta Datti Baba-Ahmed da Sanata Dabid Mark da Sanata Bukola Saraki da Gwamna Aminu Tambuwal da kuma Alhaji Kabiru Tanimu Turaki.

kokarin da Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin yake yi na zakulo mutum daya da zai fuskanci Shugaba Buhari a zaben mai zuwa bai yi nasara ba.

Haka kuma Kwamitin Walid Jibrin din bai cimma matsaya da Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na kasa (NEC) kan wurin da za a yi Babban Taron Jam’iyyar don fitar da dan takarar da za a gudanar a ranar 6 ga Oktoba mai zuwa ba.

A da dai an amince a gudanar da Babban Taron ne a birnin Fatakwal da ke Jihar Ribas inda Gwamna Nyesom Wike zai kasan ce mai masaukin baki.

Shugabannin jam’iyyar sun yamutsa fuska a wani taro da suka yi a Abuja a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da Shugaban Jam’iyyar Yarima Uche Secondus ya ce hakika a Fatakwal za a gudanar da Babban Taron, inda shi kuma Walid Jibrin ya ce ba za ta sabu ba.

Wata majiya ta ce ana jin Alhaji Walid Jibrin ya samu labarin cewa Gwamna Wike da Yarima Secondus suna kokarin bayar da tikitin takarar Shugaban kasar ne ga wani Gwamna daga Arewa idan aka yi taron a Fatakwal.

Gwamna Nyesom Wike dai ya caccaki wadansu ’yan takarar Shugaban kasa daga Arewa da suka nuna rashin yarda kan shirya taron Jam’iyyar PDP a garin Fatakwal, inda ya ce wadannan ’yan takara makiya Jihar Ribas ce da kuma Neja Delta baki daya.

Gwamna Wike ya ce, “Wadanda suke nuna rashin amincewa da gudanar da Babban Taron PDP a Fatakwal ’yan bakin cikin ci gaban Jihar Ribas da Neja-Delta ne. Idan kana nuna wa mutanen jihar da Neja Delta kiyayya a fili tun yanzu, to me za ka yi idan ka zama Shugaban kasa? Ta yaya za ka fada wa mutanen jihar da ka nuna karara ba ka son jiharsu su zabe ka a zabe? Wajibi ne mu hada kai, ba mu bukatar rabuwar kai a yanzu. Manufarmu ita ce sai mun ci zabe a 2019.”