✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben gobe: Gwamnatin Tarayya ta yi umarni a rufe iyakokin kasa

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a rufe iyakokin shigowa Najeriya saboda zaben Shugaban Kasa da Majalisar Dokoki ta Kasa a gobe Asabar. Wata sanarwa…

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a rufe iyakokin shigowa Najeriya saboda zaben Shugaban Kasa da Majalisar Dokoki ta Kasa a gobe Asabar.

Wata sanarwa da Shugaban Hukumar Shigi da Fice, Mohammad Babandede ya sanya wa hannu, ta ce umarnin ya zo ne daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau.

A cewarsa, “A shiryen-shiryen zaben gobe Asabar 23 ga Fabrailu, Ministan Harkokin Cikin Gida ya bayar da umarnin a kulle dukan  iyakokin shigowa Najeriya ta kasa daga karfe 12 na dare ranar Juma’a 22 ga Fabrailu (yau ke nan) zuwa karfe 12 na dare ranar Lahadi 24 da Fabrailu (jibi ke nan),” kamar yadda sanarwa ta bayyana.

Ta kara da cewa an dauki wannan matakin ne domin a takaita zirga-zirga a ranar zaben.