✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamna: INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta jihar Kano ta dakatar da tattara  sakamakon zaben ‘yan takarar Gwamnan Kano da aka yi ranar…

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta jihar Kano ta dakatar da tattara  sakamakon zaben ‘yan takarar Gwamnan Kano da aka yi ranar Asabar.

Kwamishinan zaben jihar Farfesa Riskuwa Arab-Shehu ne ya sanar da hakan bayan bayyana sakamakon kananan hukumomi 43 cikin 44 na jihar.

Farfesa Riskuwa, ya ce dakatar da tattara sakamakon zaben ya zama wajibi ne sakamakon rahoton kalubalen tsaro na sanar da ragowar karamar hukumar da ta rage.