✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Kogi, Bayelsa: A yau za a rufe karbar katin zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala tantance jam’iyyu 68 don yin zaben Gwamna na ranar 16 ga Nuwamba 2019 a jihohin…

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala tantance jam’iyyu 68 don yin zaben Gwamna na ranar 16 ga Nuwamba 2019 a jihohin Kogi da Bayelsa.

Hukumar INEC ta fitar da jadawalin jam’iyyun da zasu fafata a zaben 2019, wanda ta ce jami’iyyu 23 ne za su yi takarar zaben Gwamna a jihohin biyu.

A ci gaba da shirin gudanar da zaben jihohin Kogi da Bayelsa inda ake ci gaba da raba katin zabe kuwa, hukumar INEC ta sanar da cewa a yau Litinin 30 ga Satumba 2019 za a rufe karbar katin zaben da ake yi a jihohin.