✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Kogi: INEC ta bukaci a inganta tsaro

A shirin zaben Gwamnan jihar Kogi da yake karatowa ranar 16 ga watan Nuwamba 2019, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bukaci…

A shirin zaben Gwamnan jihar Kogi da yake karatowa ranar 16 ga watan Nuwamba 2019, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da an inganta tsaro kafin zabe da bayan zaben jihar.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya yi kiran yau Laraba a Lokoja babban birnin jihar lokacin bude taron horarwar kwana uku da ake yi wa jami’an tsaron da zasu yi aikin zaben Gwamnan jihar.

Kwamishinan Zabe mai wakiltar jahohin Kogi, Kwara da Nasarawa, Mohammed Kudu Haruna, ne wakilci shugaban Hukumar INEC. Ya kara da cewa, inganta tsaro na cikin samun nasarar gudanar da zabe da za a yi.