✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Kogi: INEC ta tantance Bello, Wada da ‘yan takara 49

A shirin zaben Gwamnan jihar Kogi da za a  yi ranar 16 ga Nuwamba 2019, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta sanar…

A shirin zaben Gwamnan jihar Kogi da za a  yi ranar 16 ga Nuwamba 2019, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da sunayen ‘yan takarar Gwamnan jihar 51 da aka tantance masu neman zama gwamna a jihar.

Hukumahr INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar Gwamnan da mataimakansu tare da duk bayanai game da ‘yan takarar a hedkwatar a INEC da ke Lokoja a jihar Kogi.

Wasu daga cikin wadanda aka tantance sun hada da: Gwamnan jihar na yanzu Yahaya Bello daga jam’iyyar APC sai Injiniya Musa Wada na jam’iyyar PDP.

Yahaya Bello, ya fito ne daga mazabar Okene Kogi ta tsakiya saki kuma Injiniya Musa Wada, daga mazabar Dekina Kogi ta Gabas.