✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Sakkwato: APC ta yi watsi da hukuncin kotu

Jam’iyyar APC reshen jihar Sakkwato ta ki amincewa da hukuncin karar zaben ‘yan takarar Gwamnan jihar da aka yi, inda tayi watsi da hukuncin kotun,…

Jam’iyyar APC reshen jihar Sakkwato ta ki amincewa da hukuncin karar zaben ‘yan takarar Gwamnan jihar da aka yi, inda tayi watsi da hukuncin kotun, sakamakon yin fatali da kararrakin zaben, Jam’iyyar ta APC na kalubalantar nasarar zaben Gwamna Aminu Tambuwal na jam’iyyar PDP.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Honorobul Isa Acida, ne ya sanar da hakan a yau Alhamis.

Jam’iyyar APC reshen jihar Sakkwato da Shugaban jam’iyyar na jihar duk sun watsi da hukuncin kotun, inda suka ce, babu adalci a cikin hukunci da aka zartar.