✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kano: Jibi kotu za ta yanke hukunci tsakanin Ganduje da Abba

Kotun sauraran kararrakin zaben Gwamnan jihar Kano ta sanar da ranar Laraba 2 ga  watan Oktoba 2019, a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin…

Kotun sauraran kararrakin zaben Gwamnan jihar Kano ta sanar da ranar Laraba 2 ga  watan Oktoba 2019, a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin sauraren kararrakin zaben da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar tare da dan takarar Gwamnan jihar na PDP Abba Kabir Yusuf.

PDP na kalubalantar nasarar da Gwamnan jihar na yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya samu a zaben da aka yi.

Lauyan jam’iyyar APC, Barrister Christopher Oshomegia da na PDP Barista Bashir Yusuf, duk sun tabbatarwa majiyarmu a yau Litinin hakan akan shirin da kotun ke yi na yanke hukuncin wanda ya samu nasarar zaben Gwamnan jihar da aka yi.