✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kogi: ‘Yan bangar siyasa sun babbake Shugabar mata ta Jam’iyyar PDP

Wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun bankawa shugabar matan jam’iyyar PDP ta yankin mazabar Wada/Aro, Misis Salome Acheju Abuh, wuta a gidan…

Wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun bankawa shugabar matan jam’iyyar PDP ta yankin mazabar Wada/Aro, Misis Salome Acheju Abuh, wuta a gidan ta da ke garin Ochadamu a Karamar Hukumar Ofu da ke jihar Kogi.

Wadanda ake zargin da babbake matar sun shiga cikin gidan nata ne da misalin karfe 2:00 na tsakar daren ranar jiya Litinin, inda suka kulle kowace kofar fita na gidan, daga bisani suka watsa fetur ako ina suka cinna wuta.

Ta yi kokarin ficewa daga cikin dakin amma abin ya cutura, saboda maharan sun yi ta harbi ta ko ina.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar William Aya, ya tabbatar da aukuwar hakan kuma ya yi Allah wadai da wannan mummunan aikin da ‘yan bangar siyasar suka yi.