Search
Subscribe
Zaben Malawi: An fara kidayar kuri’u 

Shugaban Qasar Malawai kuma dan takarar Jam’iyyar DPP Peter Mutharika

Zaben Malawi: An fara kidayar kuri’u 

A kasar Malawi jami’an zabe sun fara kidayar kuri’a a zaben da ake ganin mafi wuyar sha’ani a kasar wajen hasashen mutumin da zai iya lashe zaben.

Rahotanni sun ce ba a samu wasu rahotannin tashin hankali ba, kuma zaben ya kasance cikin kyakkyawan tsari.

’Yan takara bakwai ne ke fafatawa a zaben, sai dai uku cikinsu ne ake tunanin za su iya tabuka abin kirki.

Shugaba Peter Mutharika na neman wa’adi na biyu, amma Mataimakinsa Saulos Chilima da kuma Lazarus Chakwera na kalubalantarsa.

Kasar Malawin da ke Kudancin Afirka, ta dawo kan tafarkin tsarin zabe mai jam’iyyu a shekarar 1994 bayan shekara 30 na mulkin kama-karya.

Wanda zai lashe zaben na bukatar samun mafi rinjayen kuri’un da aka kada ne kawai, a maimakon samun kaso 50 cikin 100. Shugaba Mutharika dai ya lashe zaben da aka gudanar a shekarar 2014 da kaso 36.4 ne kawai.

Masu kada kuri’ar da yawansu ya tasamma kimanin miliyan bakwai, suna kuma zabar ’yan majalisa da ma shugabannin kananan hukumomi.

Wata mata a Lilongwe Babban Birnin Kasar ta shaida wa BBC cewa: “Ina matukar farin cikin in kada kuri’ata, tunda dai hakki na ne.”

Wani mai kada kuri’ar ma cewa ya yi: “Mun taru a nan ne don zabar wa kasarmu shugabanni na kwarai.”

Hukumar Zaben Kasar ta ce an dan samu tsaiko wajen bude rumfunan zaben, amma an fara zabe da misalin karfe bakwai agogon kasar, sa’a guda ke nan bayan ainihin lokacin da ya kamata a fara jefa kuri’a, inda aka bude rumfunan zaben da za su kai kaso 97 cikin 100 na runfunan zaben.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin