Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Zaben raba gardama a Kano: Yadda ‘yan daba suka cika rumfunan zabe

An gudanar da zaben raba-gardama na zaben gwamna a Jihar Kano a rumfuna sama da dari biyu da saba’in da takwas sai dai masu zabe sun kasa gudanar da zaben sakamakon cika mafiyawan rumfunan da yan daba suka yi.
A ziyarar da Aminiya ta kai mazabar Kofar Mazugal ta taras d

masu zabe sun yi dafifi a wurin inda suka shaidawa Aminiya cewa an hana su gudanar da zabe saboda da zarar sun zabi Jam iyyar PDP ake cin zarafinsu.
Malam. Dahiru Saidu ya bayyana yadda ya rasa hakoransa sakamakon zaben Jamiyyar PDP da ya yi
“Na je na kada kuriata a mazabarmu ta K/mazugal inda na zabi Jamiyyar PDP sai dai ban san hawa ba ban san sauka ba sai na ji an janyo ni an fara dukana ina juyowa sai na ga wani yaro dan Nasiru Aliko Koki da wasu mutane suka ci gaba da dukana har suka cire min hakora uku”
Aminiya ta ziyarci mazabun Nahadatu da Yalwa da Madigawa duk a Qaramar Hukumar Dala su ma wadannan mazabu cike suke da yan daba wadanda kuma ake kyautata zaton ba mazauna wurin ba ne.
Wakiliyar Aminiya ma da kyar ta sha a daidai lokacin da ake gudanar da zaben inda mamba a Majalisar Wakilai Honorabil Alhassan Yakudima ya yi umarnin da a fitar da wakiliyar Aminiya daga rumfur zaben inda ya kara da cewa babu dan jaridar da zai dauki rahoto a wurin

ADVERTISEMENT