✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Shugaban Majalisar Dattawa: Ba mu yarda da dauki dora ba – Ndume

Tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume,wanda kuma a halin yanzu yana daya daga cikin ‘yan takarar neman kujerar shugabancin majalisar karo…

Tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume,wanda kuma a halin yanzu yana daya daga cikin ‘yan takarar neman kujerar shugabancin majalisar karo na 9. Ya ce su ba za su amince da dauki dora ba, inda ya bukaci a bar dimokuraddiya ta yi aikinta. Sanatan ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi da jaridar Aminiya.

 

An gama gwagwarmayar zabe kuma ka samu nasara, sai ga shi ka sake tunkarar wani babban aikin na neman kujerar Shugabancin Majalisar Dattawa, ko me ya ja hankalin ka, ka ga ka cancanta ka nemi wannan mukami?

A matsayina na tsohon dan Majalisar Wakilai, har na tsawon shekara 8, kuma sanata mai wakiltar Kudancin Borno, na kuma fito daga shiyyar da aka bai wa dama ta nemi wannan kujera, sannan jama’ata da suka turo ni, in wakilce su, sun bani goyon baya, ko in ce sun umarce ni in tsaya, domin dalilai da yawa. Na farko dai da abu a gidan wasu gara a gidanku, idan ka duba halin da muke ciki a jihar Borno, ko kuma a shiyyar Arewa maso Gabas na kasar nan, abin akwai takaici. Kowa ya san abin da Boko Haram suka mana. Na biyu kuma mun san akidar Jam’iyar APC da kuma akidar Shugaban Kasa, kuma ina daya daga cikin wadanda ya fahimci adidarsa, sannan ina bin akidarsa tun shekarar 2002. Yanzu da Allah Ya kawo mana wannan damar, ina ganin cewa dimokuradiyya ita ce a zabe ka, ko ka zaba, shi ne nake ganin wannna damar tawa ce, kuma ta mutane Borno ce da Arewa maso Gabas da kuma Najeriya baki dayanta.

Ganin cewar ku 3 kun fito daga shiyya daya, yanzu idan uwar jam’iyya ko Shugaban Kasa suka nemi ka janye, yaya kake ganin yiwuwar hakan?

Ni kullum ina mamakin maganar janyewa, wannan fa gasa ce muke yi, maganar janye wa ma ba ta taso ba, kuma ba ya cikin tsarin dimokoradiyya. Danjum Goje da Ahmed Lawan da ni kaina, ba wanda ba zai iya zama Shugaban Majalisar Dattawa ba, kuma babu wanda ya fi wani a cikinmu, sai dai in ana maganar shekaru, to Goje ya girmemu, amma ni da Ahmed Lawan duk shekarun mu daya. Ka ga ba wani dalili da za a ce wani ya janye wa wani, zabe za a yi ba yaki ba, ko fada. Saboda haka maganar janye wa wani babu ita. Ni kuma ban nemi wani ya janye mini ba, a je a yi zabe, kamar yadda aka saba. Mun yi ma da ’yan wata jam’iyar domin kundin tsarin mulkin kasa ya amince da hakan, ba wai a yi nadi ba, ni abin da na tsaya a kai shine ban yarda da dauki dora ba, domin ya saba tsarin dimokuradiyya, kuma ba ya cikin adalci.

Ana ganin kamar ita jam’iyarku ta APC ko kuma shugabanninta sun nuna goyon bayansu ga wani bangare, ba kai ba?

A a. A bayyane take, za a iya cewa shugaban Jam’iyar APC Adam Oshiomhole ya ce suna goyon bayan Ahmed Lawan, amma ka tuna wannan ra’ayinsa ne ba na jam’iya ba. Don yin hakan ba ya cikin tsarin da jam’iyya mulkin jam’iya. Domin akwai tsari da jam’iya za ta bi, don za a ba wa kowa hakkinsa, kamar yadda doka ta tsara. APC jam’iyya ce mai adalci kuma ta haramta nuna bambamci, don yana cikin kundin tsarin mulkin kasa a sashi na 1 da 2, saboda kamar yadda ya fada na cewa, a sunan jam’iyya ko kwamitin zartarwa na uwar jam’iyya, sun ba da shawara ce, kawai tun da shi yana zaman shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, kuma shi shugaban majalisa mai barin gado ya bar jam’iyar ya koma wata, to shi a tunaninsa ba wai na jam’iya ba, sai yake ganin yin hakan ya fi, amma wannan tunaninsa ne.

Bari mu koma matsalar da ta shafi jihar ta Borno da ta tsinci kanta cikin halin kaka-ni- ka-yi na rashin tsaro da kuma ita kanta shiyyar Arewa maso Gabas.Wane tanadi kake da shi, don magance wadannan matsaloli, idan Allah ya ba ka nasara ka zama Shugaban Majalisar Dattawa?

Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa na tashi ina neman wannan kujera ta don idan Allah Ya ba ni nasara zan yi kokari wajen farfado da tattalin arzikin Borno da ma shiyyar Arewa maso Gabas da kasa baki dayanta.

Irin halin da ake ciki a Jihar Borno a yanzu haka, ya wuce duk inda mutum yake tunani. A yanzu haka Molai, Jamtilo ko Konduga ba ka isa ka shiba ba idan karfe 6 na yamma ta yi, an kone Molai Kurmus, don haka idan ba a samu shugaba wanda zai iya fito da wadannan matsaloli ba, da yanayin da ake ciki ba, kuma ya nemo taimako daga kasashen waje. Don idan kasafin da ake a kasar nan, ko kudin da Gwamnatin Tarayya za ta bayar domin sake gina jahar Borno kawai  ba zai isa komai ba. Ballantana ka yi maganar Arewa maso Gabas da ta kunshi jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da Yobe. Ba abin da kudin zai yi don irin barnar da Boko Haram suka yi wa Borno kadai zai ci Dala Biliyan 9.2 wanda idan an kwatanta da Naira ya kai Naira Tiriliyon 2.7. Idan wai za a bi ta kudin shiga da Borno take samu da wanda Gwamnatin Tarayya take ba ta, to zai dauki shekara 30, Borno ba ta dawo yadda take a da ba, ballantana a samu ci gaba. To kaga idan an samu Shugaban Majalisar Dattawa, wanda shi ne mutum na 3 a tsarin mulkin kasa, yana da dama ya yi yawo domin ya ba da wannan bayani ga duniya, don akwai masu hannu da shuni, masu son taimakawa, akwai kasashe da yawa da Allah Ya yi musu arziki suna da niyyar taimako, idan sun san halin da ake ciki, to amma ba su sani ba.To idan Allah Ya ba ni dama zan yi amfani da hakan in taimaka wajen farfado da tattalin arzikin yankin da ya lalace ga talauci, ga rashin ilimi, ga mutane na kara yawa, ga marayu na gararamba a kan tituna.

Kalubalen da mutane suke ganin za ka fuskanta shi ne tun a kwanakin baya, kungiyar Dattawan Borno da shi kansa Gwamna Kashim Shetimma sun nuna goyon bayansu ga Ahmed Lawan?

Wannan dai ba haka yake ba, cewa ya yi tunda Oshiomhole ya ce Ahmed Lawan ake so, to shi ya ba wa goyon baya, amma kar ka manta Allah shi ne mai ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya so.

Amma rashin jituwar da ka samu da Shugaban Majalisar Dattawa mai barin gado ba ka tunanin zai iya kawo maka cikas?

Ai na ce maka da Allah na dogara zai ba ni ba wani ba. Idan na dogara da wani ai imanina zai yi kadan. Don haka ni da Allah na dogara, kuma Ya ce shi yake ba da mulki ga wanda Ya so.

Ana zargin yawancin ’yan majalisa suna neman shugabancin majalisa ne saboda kudin da ke ofishin da karfin mulki?

Akwai wannan maganar. Amma yana daga cikin muraduna na neman rage karfin ofishin, inda zai zama kamar kowane dan majalisa. Hakan zai yiwu ne idan aka cire duk wani karfin iko na ofishin. Ka ga kamar Amurka da muke koyi da su, Shugaban Majalilsa bai da ko kuri’a sai dai idan an samu kunnen doki, inda sai ya zama raba gardama. Idan har Allah Ya ba ni ikon zama Shugaban Majalisar Dattawa, zan cire wasu daga cikin karfin ikon ofishin, inda zan zama kawai daya daga cikin sanatoci guda 108. Ba na goyon bayan a banbamta shugaba da sauran sanatoci. Mota iri daya za a rika hawa, kawai abin da zai bambanta mu shi ne tutar Najeriya.

Idan ka samu damar zama da sauran masu neman kujerar nan, shin za ka nemi su janye maka?

A’a. ni ba na so kowa ya janye mini. Kawai a je a yi zabe. Abin da ya kamata a yi ke nan, jam’iyya ta yi, tun a fari. Tunda mu 14 ne daga Arewa maso Gabas, kundin tsarin mulki ya yarda a ce mana ku je ku shirya tsakanin ku, ku fitar da mutum daya. Amma a ce a matsayinmu na dattawa, sannan wani mutum kuma ma daga waje, ya zo ya ce zai mana dauki-dora, idan muka yarda hakan ai ba mu wa kanmu adalci ba.

A karshe idan ’yan Jam’iyyar PDP suka nemi  ku yi hadaka domin ka cim ma burinka kamar yadda aka taba yi, shin za ka amince?

’Ya’yan Jam’iyyar PDP da suke majalisar suma ai ’yan Majalisar Dattawa ne. Babu Majalisar Dattawa ta PDP ko APC, sai dai Majalisar Dattawa ta tarayya. Yanzu idan kana neman zama shugaban mutum 108 kuma kowannensu yana da kuri’a, sai ka ce sai ’ya’yan jam’iyyarka kake bukatar kuri’arsu, kuma daya bangaren suna da kuri’a 43. Ashe kawai za ka zauna ne? ai dole ka nemi goyon bayansu. Mu ukun daga Jam’iyyar APC muke takara, wanda kuri’a 68 muke da shi. Don haka dole ka nemi goyon bayansu domin a cim ma nasara. Ko ita Jam’iyyar APC ta ba mu dama mu rika tattaunawa da su don mu samu kuri’unsu. Amma maganar a ce ka ba ni gishiri in ba ka manja, wannan ba ya cikin tsarina. Amma ina tuntubar sanatoci daga Jam’iyyar APC da na PDP.