Search
Subscribe
Zaben Shugaban Majalisar Katsina: Gwamnatin APC ta fara saka da mugun zare

Zaben Shugaban Majalisar Katsina: Gwamnatin APC ta fara saka da mugun zare

Chanji. Shi ne kalmar da jam’iyyar APC ta rika yakin neman zabenta da shi..A kawo canji shi ne abin da aka rika ikirarin za a yi idan an kafa gwamnati karkashin jam iyyar APC a jihar Katsina da ma kasa baki daya, A yakin neman zaben an rika cewa idan aka kafa gwamnati za a bar tsarin mulkin ya yi aikinsa,,ba saka hannu babu sanya baki, ba katsalandan.

An zargi tsohuwar gwamnatin PDP da babakere da handa ma da shiga sharo ba shanu a harkar duk wani reshen gwamnati da karen tsaye bisa doka. Wanda ya kawo ma kowa iya wuya kuma kowa ke jin cewa lokaci ya yi da zai samu iskar ‘yanci ya sakata ya wala. Mafarkin cewa canji zai zo kuma wani iska mai dadi zai kada.da wannnan tunani jama a sukai turuwa suka nufi fagen daga na jefa kuri a. suka kashe suka tsare suka kuma raka . Jama a sun yi jiran ko ta kwana. A kan koda an yi kokarin murde musu kuri a, sun yi niyyar sai dai ayi ta ta kare, sun rika ikirarin cewa duk wanda ya yi kokarin taba masu ‘yancin suna sun yi zaben abinda suka zaba. To tabbas. Sai dai kome ta tafasa ta kone. An yi zama na zullumi da farkagaba kowa ka gani jininsa a kan akaifa.Daga karshe aka bayyana cewa lallai. Jam’ iyyar APC ta cinye kuma ta lashe duk kujeru. Murna ta barke wasu sun mutu wasu sun kakkarye , wasu dukiyarsu ce ta salwanta. Abin da kowa ke fata wata iskar ‘yanci,mai dadi za ta rika bugawa kamar iskar safe a lokacin damina.Suna tsammanin cewa alkawuran da suka daukar ma jama a,lokacin neman kuri’arsu za su cika .
Kamar yadda suke lissafinsu daki – daki suna sauraren da wane alkawarin za a fara? Ya zuwa yanzu dai gwamnatin APC a Katsina ta saba alkawura guda uku da ta daukar ma jama a. Kamar yadda lissafi na yake tafiya, zan fadi biyu, in bar daya sai wani lokaci.Zan fadi dan karami in fadi babba kuma mafi muni.Zan bar na tsakiya sai wani lokaci wata rana. A lokacin yakin neman zabe. Malam Sabo Musa Hassan daya daga cikin jiga jigan da suka yi yakin korar PDP daga mulki,ya fada a gidan rediyon bision FM cewa gwamnatinsu ba za ta shiga sabon gidan gwamnatin da shema ya gina ba. Wanda suka kira da barnar kudi. Ya ce asibiti za a mai da shi. APC sun zagi aikin sabon gidan gwamnati suka yi kira ga jama’ar Katsina su yi Allah wadai da shi, duk wani dan Katsina y asan wannnan ya kuma ji haka. Me ke faruwa yanzu? Gwamnatin Masari daga cikin gidan take tafiyar da duk lamurranta. kila ma ta fara santin abin da ta gani a ciki.Abin takaici ko bayani har yanzu ba a yi ma ‘yan jiha me ya sa aka samu wannan canjin matsaya? Na san na daukar ma kaina duk ranar dana gwamnan Katsina koda kuwa a wajen jana’iza ne, sai na tambaye shi. Me ya sa yake zaune a cikin sabon gidan gwamnati? Duk da ikirarin APC ba zas u zauna a ciki ba? Asibiti zai zama? Mafi munin da ya faru wanda ya kamata jama’ar Katsina su fara zaman juyayi shi ne katsalandan da babakere da sa hannu da kafa da kafa idanu. Shi ne na zaben kakakin Majalisar Dokoki na jIhar Katsina. Matsayi ne mai tasiri ga ci gaban jIhar ko dakushewarta,amma yanzu sai dai mu ce a Allah YA sauwaka. Duk wata doka ta yanci an karya ta.Duk alakawarin da APC ta yi na ‘yanci da bin doka alokacin ta yi masa tsirara kuma a Majalisar Dokokin jahar. Lamarin da isar da wani irin sako ga duk wani wanda ya san abin da yake a jihar. Wannan katsalandan ya bata wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari rai. Wanda yake son ya ga jihar sa ta zama abin misali na kwaikwayo amma ta fara zama abin misali na kyama.Kamar yadda wani a fadar Shugaban kasa kuma jigo a APC ya tabbatar mana. A cikin fushi ya ce jammi’iyarsa a jiharsa kuma jihar Shugaban kasa ta fara kauce hanya.Tun kafin tsohuwar majalisa ta rusa kanta da kanta. Suka canza wani kudurin doka nasu na tafiyar da shugabancin Majalisar. Wanda yadda sukai wannan da yadda suka yi ya ba kowa mamaki. Amma an ce bukata ce daga gwamnati mai shigowa ta APC. Jaridar Daily Trust on Sunday ,14 june. Sun rubuta cewa wani ya yi masu ikirarin an bai wa tsaffin ‘yan majalisar kowa naira dubu dari biyar [500 000] domin canza waccan dokar.Zargin da tsaffin ‘yan majalisar suka karyata,amma dai sun canza dokar kwanaki uku kafin wa’adinsu ya kare. Jam iyyar APC Da gwamnatin suka zo suka yi ruwa da tsaki a zaben wanda zai sa ido ga doka ta jihar shi ne Kakakin Majalisar .Kafin zaben ,an ga wanda ake neman dorawa, yana zarya gidan Gwamnan. Har ma yana zuba ma gwamna zababbe [kafin a ranstar dashi] shayi a kofi da gyara masa takalmi idan za su fita tare.Sannan in ya yi gaisuwa a falon Gwamna ya koma gefe ya makure yana jiran umurni.
Zaben Kakakin Majalisar ba bisa ka’ida ba, yanzu har ya haifar da APC shiyyar Abuja kamar yadda aka tabbatar mani, “sam ba ayi ma Katsinawa adalci ba. Ba kuma a yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari adalci ba, kuma ba za mu zura ido hakan ta ci gaba da tafiya ba’’ inji wani dan APC Shiyyar Abuja. Me za ku yi? tambayar da na yi masa ke nna. Ba ni lokaci za ka gani a aikace inji shi, da ya roki in sakaya sunansa.
Aliyu Muduru Mani, Kakakin Majalisar ya yi karatu har digiri na biyu a kasar Malesiya. amma a Majalisar akwai wadanda suka fi shi cancanta,amma aka danne su.‘’Jam iyyar APC da gwamnatinta su sani ana kallonsu ana kuma jinsu ana kuma sane da alkawarinsu kuma za a rika tambayarsu..,,’’ inji wani da ya yi ikirarin ya karya kafa a wajen yi ma APC kamfen. danjuma Katsina.
dan jarida da ke zaune a Katsina 08035904408 email mdanjumakatsina@gmail.com

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin