Da Dumi Dumi

Zaben shugabannin majalisa: Jam’iyyar APC soja-soja ko dimokuradiyya?

Tun bayan nasarar da jam’iyyar APc ta samu a zaben Shugaban Kasa da na Majalisun Dokoki na Kasa na bana da yadda Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole  a wani taro da ya yi da sababbin zababbun ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa na jam’iyyar a Abuja, inda ya bayyana musu cewa jam’iyyar ta tsayar da Sanata Ahmed Lawan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawan a matsayin wanda zai zama Shugaban Majalisar Dattawa a zangon majalisar na 9, jam’iyyar ta afka cikin hayaniya da cece-kucen mun yarda da ba mu yarda ba.

Bayan ambato amincewa da Sanata Ahmed Lawan da jam’iyyar ta yi a waccan taro, yanzu kuma akwai rade-radi masu karfi da ke cewa jam’iyyar za ta kara matsawa gaba wajen ganin ta ba da sunan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila a matsayin wanda zai zama Shuagaban Majalisar a zangon na 9. Wadannan mutum biyu, su jam’iyyar ta APC ta ba da sunayensu don a zabe su su zama shugabannin majalisun biyu a  zango na 8, a shekarar 2015, amma wadansu ’ya’yan jam’iyyar da zuwa yanzu ta tabbata gyauron Jam’iyyar PDP ne da suka koma Jam’iyyar APC a wancan lokacin suka yi ma ta yankan baya, suka hada kai da ’ya’yan Jam’iyyar PDP, suka zabi Sanata Bukola Saraki Shugaban Majalisar Dattawa, sannan suka zabi Sanata Ike Ekweremadu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar  daga PDP.

A can ma Majalisar Wakilai haka aka yi wa jam’iyyar irin wannan tawaye, yayin da ta ce a zabi Mista Gbajabiamila Shugaban Majalisar, sai Honorabul Yakubu Dogara kamar Sanata Saraki da a shekarar 2014, suka bar jam’iyyarsu ta PDP suka komo APC, shi ma ya zama Shugaban Majalisar. Bambancin kawai da aka samu a Majalisar Wakilai shi ne yadda bayan kai-ruwa rana da nuna bacin ran shugabannin jam’iyyar ta APC, shugabanci Yakubu Dogara ya yarda an ba Honorabul Gbajabiamila Shugaban Masu Rinjaye  na Majalisar.

Idan mai karatu zai yi bitar yadda aka rika zargin shugabannin majalisun dokokin na kasa biyu, Sanata Bukola Saraki da Honarabul Yakubu Dogara kan yadda suka rika kawo tarnaki da hana ruwa gudu cikin wasu bukatun da Bangaren Zartarwa ya rika gabatar musu don neman sahalewarsu, kamar kasafin kudi da tanade-tanaden dokoki da ayyukan yau da kullum kamar na sa ido kan ayyukan Bangaren Zartarwa, kai ka san ba a yi zaman dadi ba, tsakanin Bangaren Zartarwa da na Majalisa. An yi ta kuma zargin Bangaren Zartarwar da yin ramuwar gayya wajen gurfanar da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a gaban Kotun Da’ar Ma’aikata kan tuhumar kin bayyana kadarorinsa a lokaci da bayan ya kammala wa’adinsa na shekara takwas a matsayin Gwamnan Jihar Kwara. Wannan tashin-tashin da hadamar mulki da uwa uba dama su Saraki da Dogara ba su koma APC ba sai don biyan bukatar kansu, wadda rasata da suka yi ta sa a shekarar 2018, ungulu ta koma gidanta na tsamiya, wato suka yi wa tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP kome, jam’iyyar da ake zargin tunda suka shiga APC ita suke yi wa aiki.

Da irin wannan hali na zaman doya da manja da jam’iyyar ta APC ta samu kanta kusan tsawon shekara hudun da suka gabata, tsakaninta da shugabannin majalisun dokokin biyu, da a baka ’ya’yanta ne da suka ci zabe da sunanta, amma a zuci da kuma a aikace ’ya’yan jam’iyyar adawa ne, ka iya cewa a wannan karon idan Jam’iyyar APC ta tsaya tsayin daka ta ce ga wadanda za a zaba su jagoranci tafiyar da majalisun dokokin biyu, ba ka ce ta yi laifi ba.

ADVERTISEMENT

Amma inda laifin yake shi ne na neman yin kama-karya irin ta mulkin soja, alhali ana cikin mulkin dimokuradiyya da ake sa ran duk abin da za a yi a tsaya a tattauna a ba kowa damarsa don jin irin hanzarinsa, har a samu a cimma matsayar da za ta zama maslaha ga kowa da kowa, amma sai ga shi shugabancin Jam’iyyar APC ya ki ya yi haka. Ko shakka babu dukkan wadanda ake ambato sun nuna ko za su nuna kwadayinsu na neman shugabancin Shugaban Majalisar Dattawan wato, Sanata Moharmmad Danjuma Goje (tsohon Gwamnan Jihar Gombe) da Sanata Abdullahi Adamu (tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa) da Sanata Muhammed Ali Ndume (APC Borno, wanda tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa) da shi kansa Sanata Ahmed Lawan (da bayan digirin digir-digir da yake da shi a kan yanayi, yana kuma Majalisar Dokokin tun kafuwarta a 1999), dukkansu idan ma akwai abin da ya wuce cancanta a kan jagorancin majalisar, to, suna da shi.

A can Majalisar Wakilai inda aka ce Jam’iyyar APC tana daf da bayyana sunan Femi Gbajabiamila a matsayin wanda take so a zaba Shugaban Majalisar a zango na tara, wadansu ’yan majalisar su bakwai suna can sun ja daga a kan lallai ko ana ha-maza ha-mata sai sun tsaya takarar neman mukamin Shugabn Majalisar Wakilan. Yayin da a gefe daya babbar jam’iyyar adawa tana can ta yi kwanton bauna tana zaman jiran inda za ta ga lagon Jam’iyyar APC, ta afka mata, tunda dai yaki dan zamba ne.

In da gizo ke sakar, shi ne irin yadda kawai wadansu ’ya’yan majalisun biyu ta Dattawa da ta Wakilai da sauran masu ruwa- da-tsaki na Jam’iyyar APC suke ganin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole da wadansu ’yan tsiraru na neman yi musu kama- karya tamkar ba su da damar a zauna a yi shawara da su don samun mafita. Irin wannan kama-karya ta Kwamared Oshiomhole, zuwa yanzu ita ta kara jefa jam’iyyar ga faduwa zabe a jihohi irin su Imo da Zamfara da makamantansu, faduwar da ta dauko asali tun a watan Oktoban bara da aka gudanar da zabubbukan fitar da gwanayen da za su tsaya wa jam’iyyar takara a bana, inda aka rika samun sa-in-sa tsakanin wadansu gwamnoni da shugabancin jam’iyyar a kan wa jam’iyyar za ta tsayar.

Wannan rashin dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyu mai kama da soja-soja da aka fi yi musamman a cikin jam’iyyar da ke mulki, walau a kasa ko a jiha, ya dauko asali tunda aka fara wannan jamhuriyya a 1999, yau kusan shekara 20, inda tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya mayar da tsarin cewa Shugaban Kasa shi ne uban jam’iyya, a jiha kuma Gwamna, sabanin kowa ya zama shugabancin jam’iyya ya zama abin bi sawu da kafa. A wancan lokaci ne Cif Obasanjo ya rika wasan kura da shugabannin jam’iyyarsa ta PDP irin su Cif Audu Ogbeh da Sanata Barnabas Germade da sauransu, ta hanyar sauke su ba tare da wa’adinsu ya cika ba ko sun yi wani laifi.

Tunda yanzu Jam’iyyar APC ke mulki a gwamnatin tsakiya to ya kamata ta yi kokarin kawo gyara a cikin wannan tafiya, amma ba a kullum ba a yi ta soja-soja dimokuradiyya ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya