Da Dumi Dumi

Zaben ‘yar tinke ne ko zaben kato bayan kato?

A yanzu haka dai jam’iyyun siyasa a kasar nan sun himmatu wajen gudanar da zaben fitar da ’yan takara, wato zaben fid-da-gwani, domin samar da ’yan takarar da za su fafata a zaben badi.

Sai dai kuma a yayin da jam’iyyun suka himmatu wajen wannan aikin na fitar da ’yan takara, batun  da aka wayi gari ana ta tattaunawa a kai shi ne na tsarin da za a yi amfani da shi wajen fitar da ’yan takarar, inda ake tunanin shin za a yi amfami da  tsarin fitar da dan takara na kai-tsaye (direct) ne ko kuma mai shamaki (indirect)?

Tsarin mulkin jam’iyya mai mulki, wato APC ya yi tanadin duka tsarin biyu, wanda ya sanya a halin yanzu jam’iyyar ta amince ta yin amfani da tsarin zabe kai-tsaye (wanda wadansu  a yanzu suke kira “kato-bayan-kato,”) a zaben fitar da dan takarar Shugaban kasa, a yayin da za a yi amfani da tsarin zabe mai shamaki wajen fitar da ’yan takara a sauran mukamai.

Kafin in yi bayanin kowane tsari, zan so in yi tsokaci game da fassarar tsarin zabe na kai-tsaye (direct) da wasu kafafen watsa labarai suke yi, inda suke fassara shi da “kato-bayan-kato.” Wannan fassarar tana da matsala, domin a tsarin Bahaushe a mafi yawan lokuta idan aka ce wa mutum kato to an yi niyyar kaskantar da shi ne, wato kalma ce ta kaskanci. Fassarar da magabata suka yi wa wannnan tsarin zabe shi ne “zaben ’yar tinke,” wato zaben da za a gudanar keke- da-keke, ido na ganin ido, komai a bayyane. Wannan fassarar ta fi inganci kuma ta fi mutunci.

ADVERTISEMENT

Ya kamata ma’aikatan kafofin watsa labarai su rika la’akari da cewa ba kowace kalma da ake amfani da ita a yayin zaman majalisa (wurin hira) ne za a yi amfani da ita wajen watsa labarai ba, idan wadansu wadanda ba ma’aikata ba suka fadi irin wannan kalmar kamata ya yi su gyara musu, maimaikon su taimaka wajen yayata kalmar.

Zaben ’yar tinke ya fito fili sosai ne a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarun 1990, lokacin da aka fito da jam’yyun SDP da NRC, kuma da tsarin ne aka zabi marigayi MKO Abiola a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda soke sakamakon zaben ya haifar da tashin-tashina a kasar nan.

A karkashin wannan tsari nA zaben  ’yar tinke  jama’a za su fito ne su yi layi a bayan dan takara ko hotonsa, sai a rika kidaya su daya bayan daya kuma ana fada da murya mai karfi yadda kowa zai ji, idan an kai karshen layi sai a rubuta adadin mutanen da suka zabi wannan dan takara. Haka za a yi wa kowane dan takara, a karshe sai a fadi adadin kuri’un da kowane dan takara ya samu a rumfar zaben, sai a tattara a hada da sauran sakamakon da aka samu a sauran runfuna sannan a bayyana wanda ya samu nasara.

Matsalar da ke tattare da wannan tsarin ita ce, yana da wahala a kammala zaben a tashi lafiya ba tare da hatsaniya ba, saboda a lokacin da aka shiga layi a bayan ’yan takara, magoya bayan dan takaran da ya fi mutane za su rika yi wa ’yan takarar da ba su da mutane da yawa dariya da ihu (gwalo) wanda zai iya harzuka su, daga nan sai rigima ta kaure.

Saboda haka wadansu ko da suna son dan takara idan suka ga babu mutane da yawa a bayansa sai su bar shi su koma layin dan takarar da ya fi mutane domin gudun kada su ji kunya, wato za su hakura da nagartar  dan takararsu ke nan saboda gudun tozarta, masu karfin hali ne kawai za su daure su tsaya a layi ana yi musu dariya da ihu.

Haka kuma tsarin ’yar tinke yana hana manyan mutane (su yallabai) fitowa su yi zabe, domin suna jin kunyar jama’a da sauran ’yan takara su ga wanda suke goyon baya, saboda haka sai su yi zamansu a gida su bar sauran talakawa su yi zaben. Wato dai wannan tsarin yana hana fitowar mutane sosai su yi zabe.

Shi kuma tsarin zabe mai shamaki (delegates) ana gudanar da shi ne ta hanyar wakilan da za su yi zabe a madadin sauran jama’a, shi kuma matsalarsa ita ce, yana da wahala a gudanar da zaben ba tare da murdiya ba, domin a mafi yawan lokuta ’yan takara ne ke saye masu zaben ta yadda wanda ya bayar da kudi mai yawa shi ne zai lashe zaben. Wato tsarin bai cika samar da dan takara nagari da jama’a ke so ba, hanya ce kawai ta samun makudan kudi ga wakilan da za su yi zaben. Sai dai ba a cika samun fitina ba a yayin gudanar da irin wannan zabe, domin ba a bayyane kuru-kuru ake yinsa ba kamar tsarin ’yar tinke.

Kamata ya yi a yi amfani da tsarin da ake amfani da shi wajen gudanar da zabe ne a ’yan shekarun nan, wato hadakar ’yar tinke da zabe a asirce, inda masu jefa kuri’a za su yi layi ana mika wa kowane mai zabe kati ya kebe ya zabi wanda yake so a asirce. Wannan ya fi da cewa da dimokaradiyyar kasar nan wadda har yanzu tana rarrafe ne.

Tsarin zaben ’yan takara ta hanyar tsarin wakilai (delegates) babu abin da yake haifarwa sai cuwa-cuwa da watsi da cancanta a kama mai kumbar susa.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya