Da Dumi Dumi

Zabena ba na ko a mutu ko a yi rai ba ne – Buhari

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu bukatar zabubbuka su kasance wani al’amari na ko a mutu ko a yi rai, kuma bai kamata al’ummar kasar nan su tunkari wannan al’amari cikin tsoro da fargaba ba.

Shugaban Kasar ya fadi haka ne a  jawabinsa na Sabuwar Shekara a ranar Talatar da ta gabata, inda ya nanata alkawari da kudirinsa na yin babban zaben kasar nan cikin gaskiya da adalci.

Buhari ya bayyana shekarar 2019 a matsayin muhimmiyar shekara a tarihin Najeriya, ya ce lokacin shiga kowace shekara, akan yi amfani da wannan dama wajen waiwayen baya da kuma saita alkiblar da za a tunkara a gaba.

A bana ne Najeriya za ta gudanar da zaben Shugaban Kasa da gwamnoni da kuma ’yan majalisa. “2019 za ta kasance shekarar zabe a gare mu. Nan da wata biyu za a yi zabubbuka, inda za mu zabi shugabanni a matakai daban-daban a kasa da kuma jihohi,” inji shi.

“Abin farin ciki shi ne mafi yawa na ’yan takarar Shugaban Kasa sun bayyana kudirinsu wajen tabbatar da zaman lafiya wanda kuma za mu same shi,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari ya ce shigowar sabuwar shekara, lokaci ne da ake mayar da hankali gaba. A fuskanci sababbin al’amuran da za su zo, a kuma shimfida tsare-tsare da shirya wa muhimman ranaku da harkokin da ke tafe.

“Wadanda ke ci gaba da yayata karairayi da sharrance-sharrance, don kansu, suna shure-shure ne kawai da ba zai hana su mutuwa ba. Mafi yawan ’yan Najeriya sun amince kuma suna da yakinin cewa za mu cika alkawuranmu na tabbatar da dama ta bai-daya ga kowa a zabubbuka, kuma abin da za mu yi ke nan,” inji Buhari.

Ya ce al’ummar Najeriya na muradin zaman lafiya da lumana da karuwar arziki da samun damar shiga a dama da su da bunkasa ababan more rayuwa a kasarmu da za yi alfahari da ita, a kasar nan da za ta iya tsare kanta a tsakanin kasashe.

Buhari ya nanata kudirinsa na gina kasa da za a alkinta dukiyar da Allah Ya hore mata wajen cin moriya mafi yawan ’yan Najeriya ba a raba a tsakanin ’yan tsirarun masu uwa-a-murhu da zalamar biyan bukatun kansu ba ta karewa ba.

“A kan wannan tafiya muke gaba daya, ina kuma ba ku tabbacin tsayayyen kudiri kan akidun samun kasa amintacciya da ke da tsaro da adalci da tabbatar da raba-daidai da karuwar arziki. Muna da kalubalenmu da suka shafi tsaro da tattalin arziki da siyasa da zamantakewa, amma mun kudiri niyyar yaki da samun galaba a kan dukansu,” inji Shugaba Buhari.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya