✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zai yi wuya Najeriya ta yi bikin cika shekaru 100 da samun ’yancin kai – Bisi Akande

Tsohon Shugaban Riko na Jam’iyyar APC ta Kasa Cif Abdulkareem Bisi Akande ya ce kowane dan Najeriya na zaune cikin firgici da tsoro, kuma yana…

Tsohon Shugaban Riko na Jam’iyyar APC ta Kasa Cif Abdulkareem Bisi Akande ya ce kowane dan Najeriya na zaune cikin firgici da tsoro, kuma yana da wahala kasar ta iya kasancewa a dunkule har ta iya bikin cika shekara 100 da samun ’yancin kai.

Cif Bisi Akande ya bayyana haka ne a birnin Legas a wajen bikin kaddamar da wani littafi, inda tsohon Gwamnan na Jihar Osun ya ce ana cikin wani lokaci da kasar nan take sakaci da tsarin doka. Ya ce sake tsari abu ne da ya kamata, amma kuma yana da wahala.

Ya ce dole ne sai an sake duba yadda al’amura suke tafiya a kasar nan, kamar harkar ilimi, domin tsarin iliminmu ya kasance tamkar cikin halin jahilci muke tafiya, don haka akwai bukatar a sake dubi kan lamarin. Ya kara da cewar dole ne kowane dan kasa ya kasance yana da ilimin kimiyya da sana’a domin ci gaban kasar nan.

“Sannan abu na biyu, shi ne dokokin kasar nan, domin sun kasance tamkar na soja, don haka wadannan dokoki ba za su yi tasiri a tsarin mulkin dimokuraddiya ba, muddin kuma za mu ci gaba da bin dokoki irin na soja to lallai ba za mu taba samun ci gaban da ake bukata ba,” inji shi.

Dattijo Akande ya ce lamari na uku shi ne addini, ya ce “Yadda muke mu’amallarmu ta saba da tsarin addinanmu, walau na Kirista ko Musulunci, dole ne mu kasance na kwarai a cikin dabi’unmu a ko’ina, ko a masallaci ko coci kai ko wurin bautar gumaka. Idan kasar nan ta ci gaba da kasancewa a yadda take a yanzu, ina ganin ta iya samun ta yi bikin cika shekara 60 da samun ’yancin kai, amma zai yi wahala ta cimma shekara 100 ta yi bikin ’yanci kan, muddim wadannan abubuwa uku ba a dauki matakin gyara su ba.”