✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zai zama babban kuskure idan Iran ta yi kasassabar takalar Amurka – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa kasar Iran za ta yi matukar dandana kudarta idan ta yi kasassabar kai hari a kan muradun…

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa kasar Iran za ta yi matukar dandana kudarta idan ta yi kasassabar kai hari a kan muradun Amurkar bayan da mahukuntan Washington suka jibge katafaren jirgin ruwa, mai daukar jiragen yaki a daidai lokacin da zaman tankiya ke karuwa tsakanin mahukuntan biranen Washington da Tehran.

“Za mu ga irin abin da zai faru ga Iran, idan suka kuskura suka aikata wani abu, domin zai zama babban kuskure gare su,” inji Shugaba Trump sannan ya kara da cewa “Muddin Iran ta aikata wani abu, to kuwa za ta dandana kudarta matuka.”

Kalaman na Donald Trump na zuwa ne bayan da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta bada rahoton cewa, an kai wa wasu jiragen dakon mai guda hudu hari, a ranar Lahdi, a kusa da masarautar Fujaira, wanda ke kusa da mashigar ruwan Harmouz. Sai dai Iran tana kokarin nesanta kanta daga al’amarin.

A bara ne mahukuntan birnin Washington suka janye daga yarjejeniyar shekarar 2015 da Iran ta kulla da manyan kasashen wadanda ke nufin sa ido akan shirin Nukiliyar Iran. Tun daga lokacin ne, Amurka ta kara tsaurara takunkumi a kan Iran din, tana mai cewa so take ta hana Iran fitar da manta zuwa kasuwannin duniya, kwata-kwata.

Manzon Amurka na musamman a kan kasar Iran ya ce Sakataren Wajen Amurka, Mike Pompeo ya soke ziyarar da ya shirya zuwa Moscow, a farkon makon nan, inda ya tsaya a birnin Brussels da nufin musayar bayanai ga kawayen Amurkar a nahiyar Turai da kuma jami’an kungiyar NATO, akan abin da ya kira, “yaduwar barazana daga Iran din.”