Search
Subscribe
Zakarun kulob na Turai:  Gobe za a yi wasan karshe a tsakanin Liberpool da Tottenham

Zakarun kulob na Turai:  Gobe za a yi wasan karshe a tsakanin Liberpool da Tottenham

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai da aka fi sani da (UEFA Champions League).  Wasan zai gudana ne a tsakanin kulob din Liberpool da kuma na Tottenham dukkaninsu daga Ingila a filin wasa na Atletico Madrid da ke Sifen.  Sannan za a fara wasan ne da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya.

Wannan shi ne karo na 64 tun bayan da aka fara gasar kuma yanzu shekara 27 kenan da aka canza wa gasar suna zuwa UEFA Champions League.

Tarihi ya nuna kulob din Real Madrid na Sifen ne ya fi yawan lashe wannan kofi bayan ya dauka har sau 13 sai kulob din AC Milan na Italiya wanda ya dauka sau bakwai sai kulob din Liberpool na Ingila da FC Barcelona na Sifen suka dauka sau biyar-biyar sai Manchester United wadda ta dauka sau uku.

Kulob din Tottenham bai taba daukar wannan kofi ba, hasalima wannan shi ne karon farko da ya kai wasan karshe a gasar.

Sannan tarihi ya nuna wannan shi ne karo na biyu da kulob din Ingila za su fafata a wasan karshe.  A 2008 ne  kulob din Manchester United da na Chelsea suka hadu a wasan karshe.  Haka kuma wannan shi ne karon farko a shekara 5 da za a yi wasan karshe ba tare da wani kulob daga Sifen ba.  A shekara biyar da suka wuce kulob din Real Madrid da na FC Barcelona ne suka dauki kofin a tsakaninsu.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil don ganin yadda wasan zai kaya.  Fatarmu dai a yi kallo lafiya kuma a tashi lafiya.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin