✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakarun kulob na Turai: Kwallo ta koma Ingila

A ranar 1 ga watan Yunin bana ne ake sa ran za a yi wasan karshe a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liberpool da ta Tottenham…

A ranar 1 ga watan Yunin bana ne ake sa ran za a yi wasan karshe a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liberpool da ta Tottenham dukkansu da suke Ingila a gasar Zakarun Turai.  Wasan zai gudana ne a filin wasa na Atletico Madrid da ke Sifen da misalin karfe 7:45 na dare agogon Najeriya.

Liberpool ta kai wannan matsayi ne bayan ta lallasa kulob din FC Barcelona ci 4-0 (jimilla 4-3) a ranar Talatar da ta wuce yayin da Tottenham ta kai wannan mataki bayan ta lallasa kulob din Ajad na Holland da ci 3-2 (jimilla 3 -3).

Wannan wasa ya nuna kungiyoyin Ingila ne za su hadu a wasan na karshe wanda hakan ya nuna kwallo ta koma Ingila a bana.