✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakarun Turai: Yadda wasanni na biyu na zagaye na biyu suke wakana

A ci gaba da wasannin zagaye na biyu na Gasar Kofin Zakarun Turai, ana ci gaba da yin waje da kungiyoyi da dama domin samun damar…

A ci gaba da wasannin zagaye na biyu na Gasar Kofin Zakarun Turai, ana ci gaba da yin waje da kungiyoyi da dama domin samun damar zuwa zagayen gaba, inda kungiyoyi 8 kawai za su rage.

A ranar Talata, kungiyar Manchester City ta lallasa kungiyar Schalke 04 da 7 da neam a karawarsu ta biyu, wanda ya tabbatar da wucewarta matakin dab da na kusa da karshe.

Sergio Aguero ne ya fara jefa kwallo a ragar Schalke 04 da bugun fanareti, sannan ya kara ta biyu bayan minti uku, bayan da Raheem Sterling ya turo masa kwallo da bayan kafa.

Leroy Sane ya jefa ta uku sannan kuma ya taimaka har sau uku aka ci bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, lokacin da Man City ta shiga jefa kwallaye a raga ba ji ba gani.

Sterling da Bernardo Silba da Phil Foden da kuma Gabriel Jesus dukkaninsu kowa ya ci, wanda a karshe City ta yi nasara da ci 10 da 2, a jimillar wasannin gida da waje.

A daya wasan kuma, kungiyar Jubentus ce ta yi waje da kungiyar Atletico Madrid, bayan Cristiano Ronaldo ya ci kwallo uku rigis wanda hakan ya sa Jubentus ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar.

A wasansu na farko a Madrid Atletico ce ta ci Jubentus 2 da nema, amma reshe ya juye da mujiya a wannan karawa ta Italiya, inda Jubentus ta rama biyun har ma ta dara dayar da ta ba ta nasarar zuwa matakin na gaba da ci 3-2 a jimillar gida da waje.

Cristiano Ronaldo ya ci kwallon farko ana minti 27 da wasa, sannan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci da minti hudu kacal ya kara ta biyu duka da ka.

Ana saura minti hudu lokaci ya cika na ka’idar minti 90 sai Jubentus ta samu fanareti bayan da Angel Correa ya yi wa Federico Bernardeschi keta, sai dan wasan na Portugal ya buga fanaretin ya ci.

Kwallon da ya ci na ukun ta ita ce kwallonsa ta 124 kuma karo na takwas da ya ci uku rigis a gasar Zakarun Turai.

Tashi daga wasan ke da wuya sai magoya bayan kungiyar ta Italiya sukai ta murna, su kuwa ’yan wasan na Jubentus suka yi kan Ronaldon mai shekara 34 cike da murna.

Rashin nasarar ta sa Atletico ta rasa damar yin wasan karshe na gasar ta Zakarun Turai ta bana a filinta na Wanda Metropolitano ranar 1 ga watan Yuni.

A wasannin ranar Laraba kuma, kungiyar Barcelona ce ta lallasa Lyon dad a biyar da daya a filin wasa na Camp Nou da ke Spain.

Lionel Messi ne ya bude ragar Lyon a bugun fanareti a minti 17 da fara wasa, sai Coutinho ya kara ta biyu a daidai minti 31, sai Messi na zura ta uku da a minti 78, Pikue ya zura a minti na 81, sannan Dembele ya ci ta karshe a minti 86. Ita kuwa Lyon wadda ta tashi wasan farko a Faransa 0-0, ta shi kwallo ne ta hannun Lucas Tousart a minti 58.

A karon farko na wasan, Lyon da Barcelona sun yi kunnen doki ne a kasar Faransa.

Kwallaye biyun da Messi ya ci ya sa yana da kwallo 108 a gasar cin Kofin Zakarun Turai, biye da Cristiano Ronaldo na Jubentus mai kwallo 124 jimilla.

A karon farko Barcelona za ta wakilci Spain ita kadai a karon na dab da na kusa da karshe.

Rabon da kungiya daya ta rage a gasar zakarun Turai irin wannan matakin tun bayan shekarar 2010, bayan a ranar Talata Jubentus ta fitar da Atletico Madrid a Italiya kamar yadda BBC ta rawaito.

Sai dayan wasan kuma, inda Liberpool ta lallasa Bayern Munich da ci 3 da 1 a gidan Bayern Munich. Sadio Mane ne ya zura kwallon farko a minti 26, sai Ban Dijk na kara ta biyu a minti 69, sai Mane ya rufe da kwallo ta uku a minti 84 duk da cewa Matip ya farke wa Bayern Munich kwallo daya bayan ya ci gida a minti 39.

Kungiyoyin da suka rage su ne: Kungiyar Liberpool ta Ingila da Manchester United ta Ingila da Manchester City ta Ingila da Tottenham ta Ingila da FC Porto ta Portugal da Jubentus ta Italiya da Barcelona ta Spain da kuma Ajad ta Holland.

A ranar Juma’a ce za a fitar da jadawalin wasan matakin na dab da na kusa da karshe, na kungiyoyi takwas da karfe 11 na safe.