Da Dumi Dumi

‘Zaki da Bawa’

Sallama a gare ku Manyan Gobe tare da fatar kuna cikin koshin lafiya kamar kullum. A wannan mako mun kawo muku ‘labarin zaki da bawa.’ Labarin ya kunshi yadda manyan gobe za su zama masu taimako a inda ake bukatar taimakonsu. A sha karatu lafiya:

Taku : Amina Abdullahi

An yi wani azzalumin sarki a wani kauye. Yana kuntata wa bayinsa a kullum ga shi kuma ba ya ba su abinci kamar yadda ya kamata. Abin ya ishi bayin kuma ba su san yadda za su yi ba.

Ran nan sai daya daga cikin bayinsa ya gudo zuwa daji. Ya shiga cikin wani kogo. Yana cikin hutawa sai ya ji wata kara kamar ta zaki. Waigawar da zai yi sai ya ga katon zaki jina-jina wani karfe ya shige masa kafa.

Nan take ya je ya taimaka wa zakin sai suka zama abokai.

ADVERTISEMENT

Da sarki bai ga bawansa ba, sai ya sa aka shiga nemansa har aka kama shi. Sarki ya ce zai yi masa mummunan horo saboda ya zame wa sauran bayin darasi. Sarki ya sa aka taro mutanen kauyensa, aka sanya wannan bawan a wani fili zagaye da itatuwa, sai aka sako masa zaki.

Mutanen kauyen suka zuba ido don su ga abin da zai faru. Sai suka ga zaki ya fara lashe bawan sarki. Ashe zakin da bawan ya taimakawa ne, sarki ya sa ya kashe bawa. Abin ya ba sarkin mamaki. Sai ya hakura da hukuncin kisa da ya yanke wa bawansa, ya sa aka sake shi.

Da fatar Manyan Gobe za su zama masu taimako kuma su dauki darasi a wannan labari.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya