✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Zaki da Bawa’

Sallama a gare ku Manyan Gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya kamar kullum. A wannan mako na kawo muku ‘Labarin Zaki da Bawa’.…

Sallama a gare ku Manyan Gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya kamar kullum. A wannan mako na kawo muku ‘Labarin Zaki da Bawa’. Labarin ya kunshi yadda Manyan Gobe za su zama masu taimako a inda ake bukatar taimakonsu. A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi

An yi wani azzalumin Sarki a wani kauye. Yana kuntata wa bayinsa a kullum, ga shi ba ya ba su abinci yadda ya kamata. Abin ya ishi bayin kuma ba su san yadda za su yi ba.

Ran nan sai daya daga cikin bayin ya gudu cikin daji. Ya shiga cikin kokon wani zaki. Yana cikin hutawa  sai ya ji kukan zaki.

Waigawarsa ke da wuya sai ya ga karfe ya kama wani katon zaki, inda ya yi masa jina-jina, kuma da alama zakin yana neman taimako don a kubutar da shi.

Nan take ya taimaka wa zakin kuma nan take suka zama abokai.

Da Sarki bai ga bawansa ba sai ya sa aka shiga nemansa har aka kama shi. Sarki ya ce zai yi masa mummunan horo don ya zame wa sauran bayin darasi. Sarki ya sa aka taro mutanen kauyen, aka daure wannan bawa a wani filin da aka katange sannan aka sakar masa zaki don ya cinye shi.

Mutanen kauyen suka zuba ido don su ga abin da zai faru. Sai suka ga zaki ya fara lashe bawan Sarki maimakon ya cutar da shi. Ashe zakin da bawan ya taimaka masa ne Sarki ya sa ya kashe bawan.

Abin ya bai wa Sarki mamaki. Sai ya hakura da hukuncin kisan da ya yanke wa bawan ya sa aka sake shi, don ya san ruwa ba ya tsami banza.

Da fatan Manyan Gobe za su zama masu taimako kuma su dauki darasi daga wannan labari.