✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Zaki da Zomo’

Taku: Amina Abdullahi An yi wani Zaki wanda ya kasance Sarki. Tsabagen mugunta da cin zarafi, sai ya shiga kashe sauran dabbobin ba tare da…

Taku: Amina Abdullahi

An yi wani Zaki wanda ya kasance Sarki. Tsabagen mugunta da cin zarafi, sai ya shiga kashe sauran dabbobin ba tare da sun yi wani laifi ba. Tun sauran dabbobin suna hakuri sai suka ga Zaki ya shiga kisan wadansu dabbobi wai wasa yake yi.

Ana haka har dabbobin suka ragu. Kadan din da suka rage suka zauna suka yi nazarin yadda za su bullo wa  lamarin wanda a cewarsu idan har ba a nemo mafita ba wata rana Zakin zai kashe su.

Bayan sun yanke shawarar abin da za su yi, sai suka samu Zaki suka ce da shi sun yi masa alkawarin kawo masa dabba daya a kullum domin in har ya ci gaba da kisa ba zai samu abinci a nan gaba ba. Zaki ya amince da su.     

Washegari sai aka aika Zomo ya kai kansa ga Zaki. Zomo ya dan bata lokaci kafin isarsa, yana isa sai zaki a fusace ya ce yaya aka yi ya zo shi kadai sannan ga shi dan karami?  Zomo ya ce ai sun fi haka yawa akwai wani Zakin ne da ya kame sauran ya cinye shi ma da kyar ya sha.

Zaki ya ce su je ya nuna masa. Zomo ya kai shi bakin rijiya ya ce da shi ai zakin na ciki. Zaki na lekawa sai ya ga fuskarsa a ruwa ya zaci dayan Zakin ne yana ihu sai ya ji muryarsa ta amsa ya zaci na daya Zakin ne.

Nan take ransa ya baci sai ya yi tsalle ya fada cikin rijiyar.  Daga nan ya hallaka sauran dabbobin suka samu lafiya.