✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaman cikin salama

In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa (Romawa 12:18). Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa da Yake…

In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa (Romawa 12:18).

Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa da Yake nuna mana a ko da yaushe  har Ya bamu wannan zarafi domin mu yi  bincike cikin littafinSa mai Tsarki a kan zaman salama da juna.

Zaman lafiya kamar yadda muka sani ita ce salama a takaice. Abu mafi muhimmanci da dan Adam ke bida a yau shi ne zaman lafiya. Zaman lafiya cikin zukatan mu, ko cikin iyalen mu, tsakanin mu da makwabta, tsakanin kasashen mu ko duniya ga baki daya. Amma a yau ba haka take ba, menene dalili? Rashin Kauna! Mun bar aikin halin mutumtaka ta shige gaban tafarkin Ubangiji; Galtiyawa 5:19-21 “Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da son kai, da tsaguwa, da hamayya,  da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina fadakar da ku kamar yadda na fadakar da ku a dā, cewa masu yin irin wadannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba”. Mulkin Allah na tattare da Kauna, da salama, da duk albarkan da muka gani ciki littafi mai tsarki.

Ko ina a cikin fadin duniya a yau ana ta fafutkan neman hanyar salama, yau kaji cewa shugabanin kasashe zasu hallaru a waje kaza don a tattauna yadda za a sami zaman lafiya da mafitta cikin rayuwar rashin tsaro a duk fadin duniya. A ganin ka za a iya yin haka ba tare da bin tafarkin Ubangiji ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko daya, babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah, duk sun baude, sun zama marasa amfani baki daya, babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda daya, maƙogwaronsu kamar budadden kabari ne, maganarsu ta yaudara ce masu ciwon baki ne yawan zage-zage da dacin baki gare su, masu hanzarin zub da jini ne, ta ko’ina suka bi sai hallaka da baƙin ciki ba su kuma san hanyar salama ba,  babu tsoron Allah a cikin sha’aninsu sam.” (Romawa 3:10-18 ko Ishaya 59:8) Zuciyar mutum na cike da mugunta, idan muka ce zamu nemi zaman salama da wurin ilimin ko basira da ikon kanmu ba tare da bin tafarkin Ubangiji ba to babu yarda zamu ci nasara. Shi ya sa Ubangiji Allah ya nuna mana cikin maganarSa cewa mu bidi ayukan ruhu bisa halin mu na mutuntaka domin samin nasara cikin rayuwan mu. Idan mun nemi Ubangiji da dukan zuciyar mu da dukan karfin mu, babu shakka zamu zama da kauna irin ta Ubangiji kuma salamarSa zata kasance tare da mu.

Yau idan muka duba cikin kasar mu Najeriya, zaka ji wani ya sace kudin kasa, cin hakkin na kasa da kai, cin hakkin talakawa, cin hakkin ma’aikata talakawa (kasa mai dinbin mutane kusan miliyan dari biyu), me ke kawo irin wannan? Sha’awan kayan duniya da rashin tsoro da kaunar Allah, ta wurin yin haka ne kuma akan sami rashin kauna da makwabcin ka, har ya kai mutum ga rashin samun zaman lafiya cikin rayuwan dan adam.

Kwanakin nan zamu ga cewa akwai tashe-tsahen hankali a wasu bangarorin kasan nan da dama, ta wurin nuna banbancin kabila, addini, siyasa da dai makamantansu, wannan halin kwa ta kawo mana rashin salama da juna kwarai da gaske, kwanan baya a arewa maso gabacin kasanan an yi ta fama da rashin zaman lafiya har gwamnatin tarayya ta sa wata kungiyar soji  don tsaron wannan bangare da a samu zaman lafiya, wanda a ke kira  “Operation Zaman lafiya dole”, domin tsananin irin wannan hali na rashin salama da zaman lafiya ya sa zaman lafiya ta zama “dole”. Zaman lafiya ba abu ne da sai an tilasta maka ba idan kana da kauna da kuma tsoron Allah a zuciyarka, abu ne mai sauki idan muka bi tafarkin Ubangiji Allah – mu ji tsoron Sa mu kuma kaunace Shi da dukkan ranmu da karfin mu, idan har muka yi wannan babu shakka bazamu sami matsala ba wajen nuna irin wannan hali ga junan.

Sai mu guje wa ayyukan jiki da sha’awace-sha’awcen ta mu nemi albarkar ruhu maitsarki, domin sha’awan ayukan jiki ne ke kawo mana rashin salama da zaman lafiya da juna. Littafin Yakubu 4:1-4 na cewa; Me yake haddasa gāba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba? Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisankai. Kukan yi kwadayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da fada. Kukan rasa don ba kwa addu’a ne. Kukan yi addu’a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku batar a kan nishadinku. Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan”. A nan mun dai ga hanyar da Ubangiji ya nuna mana cikin maganarSa, son duniya kan kai mu ga wahala, rashin salama da zaman lafiya kamar yadda muke fuskanta a yau, amma abin farin ciki shi ne, Ubangiji ya nuna mana mafita; mu nemi albarkar ruhu maitsarki don tafiyar da rayuwan mu a nan duniya, salamar Ubangiji Allah kuma zai kasance tare da mu.

Filibiyawa 4:6,7; “Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roƙo, tare da gode wa Allah.  Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu”. Bari salamar Ubangiji Allah ta kasance cikin zukatan mu, amin.