Zaman tankiya a Gabas ta Tsakiya bayan harin da Amurka ta kai a Iraki

Kimanin mayaka 25 ne suka mutu lokacin da Amurkar ta kai wasu hare-hare kan sansanin mayaka masu alaka da kungiyar Kataib Hezbollah a Iraki da Syria.

Amurka ta ce ta kai harin ne a matsayin ramuwar gayya kan harin da Iraki ta kai mata ranar Juma’a wanda ya yi sanadiyyar halaka wani Baamurke. Firai Ministan Iraki Adel Abdul Mahdi ya ce hare-haren ta sama sun keta ikon da kasarsu ke da shi yana mai cewa hakan zai sa su sake yin nazari kan alakarsu da Amurkar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, jiragen yakin Amurka suka yi luguden wutar da ya kashe mayakan Hezbollah 25, farmakin da ake kallo a matsayin ramuyar gayya kan jerin hare-haren rokokin da suka yi sanadiyar mutuwar wani Ba’amurke guda a Iraki.

…martanin kasashen duniya kan harin 

Iraki ta yi gargadin ‘mummunan sakamako’ zai biyo baya. Firai Ministan Iraki, Adel Abdul Mahdi ya yi Allah wadai da hare haren, ya kuma yi gargadi cikin kalamansa cewa matakin na Amurka ba za su yarda da shi ba kuma akwai mummunan sakamako.

ADVERTISEMENT

“Ya kwatanta harin a zaman wani mugun abu da ba za a taba yadda da shi ba; wanda zai iya haifar da mummunan martanin,” kamar yadda wani jawabi daga ofishinsa ya nunar.

…Rasha ta soki lamirin harin a zaman abinda ba za a taba yadda da shi ba

Ma’aikatar wajen Rashar ta bayyana “musayar hare-hare tsakanin Hesbollah da dakarun na Amurka a zaman ‘abin da ba za a taba amince wa da shi ba’, ta kuma yi kiran da a kai zuciya nesa daga dukka bangarorin biyu.

…Syria ta yi gargadin Amurka game da tsoma baki a harkokin cikin gidan Irakin

Syria ta caccaki harin a yankin, tare da nuna goyon bayanta ga al’ummar Irakin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SANA ya ruwaito.

Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar y ace Syria tana nuna cikakken goyon bayanta ga al’ummar Irakin da kuma kafofin gwamnatin kasar, tana kuma jan kunnen da ta daina katsalandan game da harkokin cikin gidan Irakin.

…Isra’ila kuma ta yi na’am da harin kan Iran da kuma ’yan korenta’

Firai Ministan Isra’ilan Benjamin Netanyahu ya ce yana taya murna ga Sakataren Wajen Amurka Mike Pompeo “kan muhimmin farmakin da Amurkar ta kai kan Iran da ‘yan kanzaginta a yankin”. Kamar yadda jaridar Jerusalem Post ta nunar.

…..Iran ta soki Amurka game da mara baya ga ‘ta’addanci’

Iran, wacce ta musanta hannu kan harin da aka kai wa dakarun Amurkar, ta soki harin da Amurkar ta kai a zaman na “ta’addanci”.

“Wannan ikirarin da Amurkar ta yi ba tare da wani kwakkwaran shaida ba, ba hurumi ba ne da zai sa a kai harin bom tare da kashe mutane wanda hakan keta haddin dokokin kasa da kasa, kamar yadda kakakin gwamnatin Iran din Ali Rabiei ya nunar.

“Harin ya kara tabbatar da karyar da Amurka take yi kan yaki da kungiyar Daesh … sakamakon yadda ta kai hari kan dakarun da suka dade suna yakar kungiyar ta Daesh,” inji Abbas Mousabi kakakin ma’aikatar wajen kasar.

Ya kara da cewa kasancewar dakarun kasashen waje a yankin shi ne dalilin karuwar rashin tsaro da kuma zaman tankiya a yankin. “Don haka dole Amurka ta kawo karshen mamayar da take yi a yankin,” inji shi.

…Kungiyar Kataib Hezbollah ta ce ‘yanzu an bude babin yaki da Amurka gadan-gadan’

Ta cikin wani jawabi, kungiyar ta ce yanzu ne za ta fara yaki da Amurka gadan-gadan.

“Yakinmu da Amurka da ma ‘yan korenta, a yanzu mun bude shi ta yadda komi ma ka iya faruwa,” a cewar wani kakakin kungiyar.

“A yau ba mu da wani zabi da ya wuce mu yi fito na fito da Amurkar; kuma babu abinda zai hana mu mayar da martani game da wannan danyen aikin.”

…Jagora Ayatollah Ali al-Sistani ya koka ‘keta haddin’

Babban jagoran Shia a Irak ya yi kira ga gwamnatin Irakin da ta tashi tsaye wajen kare kasar daga ‘afkawa a zaman fagen bai wa hammata iska tsakanin manyan kasashen yankin da kuma na duniya baki daya’.

Cikin wata sanarwa, Babban Jagora Ayatollah Ali al-Sistani ya soki lamirin abinda ya kira “keta haddi da takalar fada” da Amurka ta yi tare da yin kiran Amurkar ta martaba diyaucin kasar Irakin ta kuma guje wa haike wa yancin Irakin da sunan “wai tana mayar da martani kan aikace-aikacen wasu kungiyoyi na daban.”

Al-Sistani, ya kuma kara da cewa “mahukuntan Irakin ne kawai ke da hakkin daukar mataki kan irin wadannan kungiyoyin, tare da daukar matakan yi wa ayyukansu birki.”

Sai dai ana ganin kalaman nasa a zaman wani gargadi kan yiwuwar duk wani martanin da kunyoyi masu samun goyon bayan Iran ka iya mayar wa.

…Dakarun Popular Mobilization Forces sun yi barazanar ‘mummunan martani’ kan dakarun Amurka

Wani Babban kwamandan mayakan Jamal Jaafar Ibrahimi,da aka fi sani da Abu Mahdi al-Mohandes, ya yi alwashin daukar fansa kan dakarun Amurka a Iraki.

“Martaninmu zai zama mai zafin gaske kan dakarun na Amurka a Irakin,” inji Mohandes.

Mohandes dai babban kwamanda ne na kungiyar ta PMF a Iraki, wadda wani reshe ne na kungiyoyin mayaka da galibinsu masu dauke da makami ne ’yan Shia da ke samun tallafin kasar Iran; an kuma surka mayakan cikin dakarun gwamnatin Iraki.

Ya kuma kasance wani jigo daga cikin  kawayen Iran a Iraki, ya kuma taba zama jagoran kungiyar Kataib Hezbollah, wacce ya kafa da kansa.

…Masu zanga-zanga sun kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Iraki

Dubban masu zanga zangar sun yi dandazo a wajen ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza, domin nuna bacin ransu game da hare-hare ta sama da Amurkan ta kai kan mayaka a Iraki masu samun goyon bayan Iran. Sun yi tattaki zuwa ofishin kuma cikin fushi suna fadin “Mutuwa ga Amurka’’ tare da kona tutocin Amurkar.

Ma’aiakatar tsaron Amurka Pentagon ta tura sojin kundumbala guda 100 zuwa ofishin jakadancin Amurkar a birnin Baghdad domin kara samar da tsaro a ofishin bayan da a ranar Talata daruruwan masu zanga-zangar da suke goyon bayan Iran suka afkawa ginin inda suka cinna wuta kan ginin domin nuna bacin ransu dangane da harin na Amurka.

Sai dai sojin Amurkar da ke cikin ginin a lokacin sun yi ta harba hayaki mai sa kwalla da jefa gurneti tare da harbin irin na gargadi kan masu zanga-zangar inda suka raunata 62 cikinsu. Masu zanga-zangar sun yi nasarar cinna wuta a dakin karbar baki na ofishin.

Sai dai jakadan Amurkar yana hutu a daidai lokacin da aka far wa ofishin nasa, an riga da an dauke ma’aikatan ofishin a lokacin gabanin harin ya rutsa da sojin kundumbalar Amurkar wadanda suka samu kariyar gilashin da harsashi baya huda shi na ginin.

Sakataren Tsaron Amurkar Mark Esper ya ce suna shirin aika karin dakaru zuwa ginin jakadancin; yayin da yake kiran Irakin da ta taimaka wajen kare rayukan Amurakawa a kasar, sa’o’I kalilan bayan da Shugaba Trump ya soki lamirin Irakin game da harin inda y ace ‘za a dora laifin harin ne kacokan kan Irakin’.

A karon farko kenan cikin tsawon shekaru da masu zanga-zangar suka samu damar isa ofishin jakadancin Amurka da ke wani yanki mai cike da tsaro, na Greenzone inda suka tsallake shingayen binciken ababen hawa. Wani dandazon maza sanye da kakin soja da kuma ayarin mata sun yi tattaki har zuwa katanagar ofishin jakadancin ba tare da wani jami’in tsaro ya dakatar da su ba.

Masu zanga-zangar sun yi ta cilla duwatsu, yayin da suka banbare kyamarorin da aka makala a jikin ginin ofishin jakadancin na Amurka.

…Amurka ta yi gargadin yiwuwar sake kai hari

Amurka ta kare hare haren da ta kai din tare da yin gargadin cewa za ta iya sake kai wani harin, duk da irin sukar da ta biyo baya daga kasashen duniya da kuma sabuwar barazana daga mayakan kansu.

“Ba zamu bari Iran ta yi amfani da wasu mayaka don su kai hari akan muradun Amurka,” wani babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ya fadawa manema labarai, yana bayyana hare haren a matsayin na kariya.

Share