✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamanin labaran karya, bukatar a yi hattara

A sakamakon shigowar kafofin watsa labarai ta hanyar shafukan sada zumunta yanzu yada labaran karya ya zama ruwan dare ta yadda sai an yi da…

A sakamakon shigowar kafofin watsa labarai ta hanyar shafukan sada zumunta yanzu yada labaran karya ya zama ruwan dare ta yadda sai an yi da gaske kafin a iya magance matsalar.

Kafin zuwan kafofin sada zumunta, kafofin watsa labarai irin su rediyo da jaridu ne aka fi dogara da su wajen samun labarai, amma yanzu kafar sadarwa ta sada zumunta ta mamaye harkar sadarwa ta yadda hatta kafafen watsa labarai ma suna amfani da wannan hanyar wajen samun labaran da za su yi amfani da su.

Kasancewar kowa yana yada abin da ya ga dama ta hanyar kafar sada zumunta, yanzu kowa ya zama dan jarida, wanda ya sanya aka wayi gari kowa yana watsa labaran da ya ga dama ba tare bin ka’ida ba.

Aikin watsa labarai yana da ka’idoji amma mafi yawan wadanda suke yada labarai ta kafofin sadarwa ba su sansu ba, shi ya sanya yada labaran karya ya zama ruwan dare a yau, musamman da yake yana da wahala hukuma ta kama wanda ya kirkiri labarin karya ya watsa kuma sauran mutane suka ci gaba da yadawa.

Wani lokaci labarin da aka kirkiro sai an yi da gaske za a iya gane cewa karya ne, saboda labari ne mai dauke da hoton bidiyo da ake ji kuma ake gani. Misali labarin auren da aka ce Shugaban Kasa Buhari zai yi da ministarsa Sa’adiyya Umar Farouk, wanda aka nuna hoton bidiyo na Sa’adiyya a matsayin amarya tana shirin biki, ga mata nan kewaye da ita a cikin yanayi na shagali. Sannan ga katin gayyatar daura aure an buga, inda aka sanar da rana da wurin da za a daura auren. Tun ana daukar labarin a matsayin tatsuniya har mutane suka fara tunanin lallai labarin akwai kanshin gaskiya, amma daga baya sai aka gane cewa duk shiri ne kawai.

Haka kuma an kara wa labarin auren karfi inda aka nuna Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari a fadar gwamnati tana taratsi saboda an rufe mata kofa, kuma aka ji wata mata tana ba ta hakuri tana cewa ‘Gwaggo wallahi babu wanda ya fada mana za ki zo,’ an nuna wannan bidiyo ne a daidai lokacin da A’isha Buhari  take kasar Ingila, wanda ya sanya ake yada labaran cewa ta yi yaji ne saboda za a yi mata kishiya, saboda haka wannan bidiyon da aka watsa kwana guda kafin ranar da aka ce mijinta zai kara aure, sai ya nuna kamar A’ishar ce ta dawo babu shiri saboda ta ji mijinta zai kara aure washegari, domin haka ta dawo Fadar Shugaban Kasa a fusace tana fada.

Amma daga bisani sai aka gane cewa ba haka ba ne, domin A’isha Buhari ba ta dawo Najeriya ba a wannan lokaci, sai bayan kwanaki biyu. Kuma ita A’isha Buharin ta bayyana cewa lallai ita ce a wannan bidiyo amma  an dade da daukarsa. Jingina shi da aka yi da labarin kara auren Shugaba Buhari ya sanya wadansu sun yarda cewa lallai maganar auren akwai kanshin gaskiya domin ga shi ita kanta Uwargidan Shugaban ta rikice.

Wannan lamari da ya faru game labarin kara auren Shugaba Buhari ya nuna cewa al’amarin labaran karya ya kai kololuwa, sai an yi da gaske za a iya shawo kansa,.

A shekarun baya ma haka wata ta watsa labarin cewa idan aka yi wanka da ruwan gishiri kuma aka sha za a tsira daga cutar Ebola (saboda a lokacin cutar tana ta kashe mutane), kuma a wannan daren za a yi, kada a bari alfijir ya fito. Hakan ya sanya labarin ya watsu kamar wutar daji, aka rika layi a gidajen haya saboda a yi wanka da ruwan gishiri kafin gari ya waye, har dambe aka rika yi saboda lokaci zai kure wadansu ba su samu shiga bayi ba. Daga baya aka gane cewa labarin karya ne, wata ce kawai ta kirkiri labarin da wasa ta tura wa wadansu a matsayin raha, amma labarin ya watsu nan da nan, daga bisani ya yi sanadiyyar tayar wa mutane masu hawan jini da ciwonsu, wadansu kuma suka rasa rayukansu. Illar yada labarin karya ke nan.

Akwai bukatar gwamnati ta himmatu wajen magance wannan matsalar ta labaran karya domin idan ta yi sakaci za a kai lokacin da shugabancin jama’a zai gagara saboda jita-jita ta samu wurin zama.

Ya kamata su kuma masu yada labaran karya su kula, idan sun dauka abin wasa ne ko na nishadi ne, to su sani wadansu ba za su dauki labarin da wasa ba, kuma irin wadannan labaran suna iya haifar da yaki a kasa da sauran fitinu iri-iri.

Su kuma sauran mutane su daina saurin amincewa da labari sai sun bincika, domin duk wanda ya taimaka wajen yada labarin karya duk fitinar da labarin ya jawo shi ma yana da kamasho. Allah Ya kyauta Ya kuma kiyaye.