Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Zan amince da sakamakon zabe mai inganci – Atiku Abubakar

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai amince da sakamakon zabe ko da kuwa an kayar da shi matukar an gudanar da zabe mai inganci.

Atiku ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi tare da dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na PDP, Peter Obi a tattaunarsu da fitacciyar ’yar jaridar nan Kadaria Ahmed a shirin nan ’Yan Takara a Abuja a shekaranjiya Laraba.

ADVERTISEMENT

Atiku ya ce lallai yana da duk abubuwan da mutum ke bukata domin ya zama Shugaban Kasa, musamman idan aka yi la’akari da yadda wannan gwamnatin ta gaza.

Da Kadaria ta tambayi Atiku ko zai amince da sakamakon zaben, sai ya amsa da cewa, “Idan an gudanar da zabe mai inganci, zan amince da sakamakon. Na sha faduwa a zabe.”

ADVERTISEMENT

Game da yaki da cin hanci, sai tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce zai yi wa lamarin gyaran fuska, “Na riga na bayyana yadda zan tsabtace yaki da cin hanci. Dole lamarin ya kasance an gajarta lokacin bincike.” Da ta sake tambayarsa yaya zai yi hakan ya yiwu, sai ya kara da cewa, “Dole a samar da doka da za ta tabbatar da hakan. Najeriya kasa ce da ke da doka. Don haka dole a samar da doka.”

“Abin da nake nufi shi ne dole a ba hukomomin bincike lokacin da za su dauka wajen bincike, sannan a samar da lokacin da ake bukata domin tuhuma tare da hukunta wanda aka samu da laifi,” inji shi.

Atiku ya kara da cewa idan har wasu kasashe za su dauki dan lokacin wajen gabatar da bincike tare da yanke hukunci a kan cin hanci, Najeriya ma za ta iya.

Haka kuma a batun yin sulhu da wadanda suka kwashi kudin gwamnati, Atiku ya ce zai iya yin sulhu da su idan suka dawo da kudaden da suka diba, “Zan ba ki misali da kasar Turkiyya. Turkiyya ta sanar da yin sulhu ga barayin gwamnati, wanda hakan ya sa duk kudaden da suke kasashen waje  aka dawo da su. Kalli yadda Turkiyya ta zama yau, tana iya hada kafada da duk wata kasa a Nahiyar Turai. Sannan daga baya ta ja layi a kan cin hancin. Ina da tunanin yin irin haka,” inji shi.

Sannan Atiku ya ce zai samar da Hukumar Sauraron Laifuffukan Zabe, wadda za ta rika ladabtar da duk wadanda aka kama da kowane laifi da ke da alaka da zabe, kamar magudin zabe da sauransu, ko da kuwa wakilin jam’iyya ne ko jami’in Hukumar INEC ko jami’in tsaro

Game da batun Boko Haram kuwa, Atiku ya bayyana cewa zai karfafa sojoji da duk abin da suke bukata, kuma zai rika bincikar manyan sojojin a kan yadda suke gudanar da ayyukansu, “Amma kuma idan na yi maka duk abin da kake bukata, sannan ka ki yin aikinka, to zan yi maganinka,” inji Atiku.

…Atiku ne wanda zai iya hada kan mutanen Najeriya – Peter Obi

A jawabin dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa, Peter Obi ya ce lallai Atiku Abubakar ne wanda zai iya hada kan Najeriya.

“A wannan lokacin da muke ciki, muna bukatar wanda yake da ilimin yadda za a hada  kan kasar nan,” inji shi.

Game da batun yaki da cin hanci, shi ma ya ce, “Kamar kana da tattalin arzikin Dala biliyan 520 ne sai ka bar shi, ka koma kana bin barawon da ya sace kudin, sai ka kwato Dala 5 kawai. Wannan ai ba riba. Kuma ki tuna fa a jerin kasashen da suke cin hanci, Najeriya ce ta 136, daga baya ta koma ta 148, sannan kuma ta sake dawowa ta 144. Wannan ci gaba ne?”