✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan bar sana’ar waka bayan na yi aure –Mawakiya Fatima Umar Lema

Daya daga cikin mawaka mata da ke tauraronta ke haskawa a Jihar Sakkwato Fatima Lema ta ce bayan ta yi aure ba za ta ci…

Daya daga cikin mawaka mata da ke tauraronta ke haskawa a Jihar Sakkwato Fatima Lema ta ce bayan ta yi aure ba za ta ci gaba da yin sana’ar waka ba.

Fatima ta bayyana wa Aminiya a Sakkwato haka ne lokacin da yake tattaunawa da ita a ranar Litinin da ta gabata.

Fatima Lema ta ce ba ta da ra’ayin na bayan aure ta rika fita yin waka a situdiyo kamar yadda wadansu mata mawaka ke yi, inda ta ce tana ganin hakan ya saba wa tarbiyyar da aka koya mata a gidansu kan abin da ya shafi zaman gidan miji.

Mawakiyar da a Sakkwato ake yi wa kirarin da mai makoshin zinare ta ce waka sana’a ce babba matukar mawaka sun rike ta da muhimmanci. “Mu mawaka ya kamata mu riki sana’armu da girma da daraja, sannan akwai bukatar mu hada kanmu wuri daya tare da daina kyashin juna. Abin da muke yi fadakarwa ce ga jama’a, don haka ne ya kamata a rika koyon alheri a wajenmu,” inji ta.

A bangarorin nasarorin da ta samu a harkar waka, Fatima cewa ta yi, “Na samu nasarori sosai a harkar waka, domin a gaskiya na mallaki abin da ban zaci zan iya samu ba a duniya. A tsarina ba na yanke farashi idan zan yi wa mutum aiki, kawai duk abin da ya ba ni zan karba in yi tafiyata, sannan kawayena in za su yi aure nakan yi musu waka kyauta.”

Da aka tambaye ta ko mene ne dalilin da ya sa ba a cika jin wakokin mawaka mata ’yan asalin Jihar Sakkwato a wajen jihar ba, sai Fatima ta ce rashin rashin daukar sana’ar da muhimmanci da rashin hadin kai ne yake damunsu, “Rashin hadin kai ne da kuma yadda ba su dauki aikin kamar yadda maza suka dauke shi ba, muna da matsala ta wasa da aikin har ya kai aka daina nemanmu don gudun kawo cikas ga aikin. Za ka ga mace a nan kowa yana son in ya zo daga Kano ko Kaduna ko Jos yin wani aiki ta yi masa amshi ko su yi wakar tare, amma sai wani lokacin a yi ta nema a rasa ko a same ta, amma ba lokaci, ka ga dole a kyale su.”

A bangarorin yawan wakokinta kuwa cewa ta yi, “A yanzu ina shirin fitar da kundin wakokina na saurare domin duniya ta kara sanin Sakkwatawa mata suna iyawa, kawai jan kafa ne suke yi ba su daukar abin da zafi,” inji ta.

Ta ce ba ta san yawan wakokin da ta yi ba, domin tana yin kowace irin waka kuma a kowane fanni kamar wakar sarauta da soyayya da aure. Sannan ta ce ta rubuta wakoki akalla 30 da hannunta.

Da aka tambaye ta abin da ya fi ba ta wahala a waka sai ta ce, “Murya ta kasa a karshen zango, da a jiye murya domin zubi-zubi ne, kuma wakoki sukan zo da yanayi daban-daban kuma kowane lokaci akwai muryar da ake bukata tare da kai wani lokacin ka nemi muryar ka rasa samu. Amma abin da ya fi burge ni a waka shi ne salo da fadakarwa da dadin wakar da mawaki ke yi.”

Fatima ta ce ta yi karatunta na firamare da sakandare da Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari duk a Sakkwato kuma ba ta taba barin jihar zuwa wata jiha yin aiki ba.

Ta ce ta shigo harkar waka ta sanadiyar wani dan uwanta Hali Korosa saboda sha’awar da take da ita na a ji muryarta kamar yadda take jin muryar wadansu a fina-finan Hausa, “Lokacin da na fara amshin waka ina jin tsoro don ko gidanmu ba a sani ba, amma a nan na ga abin mamaki in da kowa ya yi farin ciki da muryata da ya ji, inda a nan ne fa aka rika kirana ana ba ni aiki har na samu daukaka da farin jini a cikin al’umma,” inji Fati Lema.