Da Dumi Dumi

Zan bunkasa ci gaban mata da matasa – Aliyu Mathias

Aliyu Mathias

Kansilar Mazabar Wuse a Karamar Hukumar Birnin Abuja, Mista Aliyu Mathias ya ce zai ba da himma wajen bunkasa ci gaban mata da matasan mazabarsa domin inganta rayuwarsu.

Aliyu Mathias ya ce samar wa matasa guraben ayyukan yi na daya daga cikin abubuwan da zai fi bai wa fiffiko a zangon mulkinsu. Ya ce matasa su ne gimshikan ci gaban kowace al’umma don haka ba za a bar su kara zube ba, dole a koya musu sana’o’i.

Mathias ya ce yana da burin ganin matasan yankin Wuse sun yi fice wajen samun tallafin karatu da ba su kayayyakin sana’a bayan an koya musu duk sana’ar da mutum yake da niyyar koya. Ya ce hakan ita ce hanyar da za a raba matasa da munanan dabi’u na shaye-shaye da sauransu.

“A bangaren mata kuwa akwai shirin na musamman na tallafa wa mata masu juna biyu da masu shayarwa ta hanyar ba su tallafin kayan haihuwa da taimakawa a asibitoci da kuma ba da himma wajen kula da lafiyar jarirai, kuma da koya wa su kansu matan sana’o’i da ba su jari da kayan aikin  don aiwatar da abin da suka koya. Sai ya yi kira ga al’ummar mazabarsa ta Wuse su ba shi hadin kai da goyon baya domin samun nasara.

ADVERTISEMENT
Share