Search
Subscribe
Zan bunkasa ilimi da koya wa matasa sana’o’i a mazabata – Maitala

Alhaji Haruna Maitala jingir

Zan bunkasa ilimi da koya wa matasa sana’o’i a mazabata – Maitala

Zababben dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato, Alhaji Haruna Maitala Jingir ya ce zai mayar da hankali wajen bunkasa ilimi da koya wa matasa sana’o’i a mazabarsa.                                                                                                                                             Alhaji Haruna Maitala Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Jos, inda ya ce zai mayar da hankali wajen ganin  yara sun  yi karatu a mazabar kuma zai taimaka wajen ganin matasan mazabar sun koyi sana’o’in hannu kamar gyaran motoci da walda da kafinta da sauransu.

Ya ce idan aka bunkasa ilimi aka samar da ayyukan yi ga matasa, za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a mazabar da kasa baki daya.

Alhaji Maitala ya yi bayanin cewa zai hada hannu da jami’an tsaro da sauran al’ummar mazabar,  wajen ganin an samu tabbatatcen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin