✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan ci gaba da yin fim a wajen Kano-Naburuska

Fitaccen jarumin Kannywood Sharu Mustapha Naburuska ya ce ya yanke shawarar ci gaba da yin fim a wasu jihohin wajen Kano. Naburaska ya yi wannan…

Fitaccen jarumin Kannywood Sharu Mustapha Naburuska ya ce ya yanke shawarar ci gaba da yin fim a wasu jihohin wajen Kano.

Naburaska ya yi wannan bayani ne bayan ya shelanta ficewarsa daga masana’antar a makon jiya, bayan Naburuskan ya zargi Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano da kokarin durkusar da harkar fim, ta hanyar fakewa da wasu abubuwa tana cin zarafin ’yan fim wadanda ba su tare da gwamnati.“Mun san wannan kamen da ake ta yi siyasa ce domin zuwa yanzu akalla an kama mutum biyar wadanda duk magoya bayan Jam’iyyar PDP ne, amma har zuwa yanzu ko mutum daya ba a kama ba daga bangaren APC. Kuma kowa ya san cewa suna aikata laifuffuka. Akwai mawakin da ya yi wakar ‘Malam ya ci kudin makamai da ‘Ka bi ubanka kai Abba!” Da sauran wakoki na cin mutuncin mutane. A fahimtata ana fakewa ne da Masana’natar Kannywood a ci mutuncin mutane,” inji shi.

Ya ce “Ina so jama’a su fahimci cewa ba wai na bar fim ba ne, don ina tsoron kada Hukumar Tace Fina-Fnai ta kama ni, illa don wadansu mutane masu daraja da suka ga dacewar in yi hakan din. Ba na tsoron kamu ko dauri, domin ni namji ne, mace ma tana zaman gidan kaso ballantana namji.”

Naburuska ya ce Hukumar Tace Fina-Fina ta Jihar Kano ba ta da alaka kai-tsaye da dan fim haka ba ta da hurumin gurfanar da wani dan fim gaban jami’an tsaro ko  kotu. “Ita wannan hukuma da dokokinta duk zuwa suka yi suka same mu a wannan masana’anta, don haka mun san duk abin da dokar ta kunsa. Dokar ba ta ba hukumar damar yin kame ba, ballantana ta gurfanar gaban kuliya. Dokar ta ba hukumar damar gayyato duk wanda ya fitar da fim ba tare da ya cire abin da aka umarce sh ya cire ba wajen tacewa ba, tare da hukunta shi ta hanyar cin tararsa wasu kudade don ya zama darasi gare shi da sauran abokan sana’arsa,” inji shi.

Jarumin ya ce hukumar ba ta da ruwa a harkar Intanet, saboda Intanet abu ne na duniya gaba daya. Ya yi kira ga masoyansa cewa su yi hakuri game da matakin da ya dauka inda ya ce na dan lokaci ne. “Ina ba masoyana hakuri amma komai yana da iyaka zan dawo Kano in ci gaba da harkokina idan wannan gwamnati ta sauka. Kuma ina sanar da su cewa za su ci gaba da kallon fina-finaina duk da cewa ba a Kano za a sake shi ba amma hakan ba zai hana su mallakar fina-finan ba,” inji shi.

Jarumin ya ce sakamakon ficewarsa daga harkar fim a yanzu haka har wata kungiya mai zamna kanta wacce ke fafutikar wanzar da zaman lafiya a kasar nan ta ba shi mukamin mai magana da yawunta a Arewacin Najeriya, inda yake ganin hakan a matsayin ci gaba a gare shi.