✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan dakile bangar siyasa  – Bashir Matawalle

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Argungu da Augi, Alhaji Bashir Isah Matawalle ya bayyana wa Aminiya wasu shirye-shirye da yake da su don ceto…

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Argungu da Augi, Alhaji Bashir Isah Matawalle ya bayyana wa Aminiya wasu shirye-shirye da yake da su don ceto rayuwar matasan mazabarsa daga zaman kashe wando da shaye-shaye da kuma bangar siyasa da kuma  samar musu da sana’o’i:

Mene ne cikakken sunanka?

Sunana Bashir Isah Matawalle kuma ina wakiltar Argungu /Augi a Majalisar Wakilai  kuma wannan ne karo na farko da na fara zuwa majalisa.

Kafin ka zo majalisar wadanne  mukamai ka taba rikewa a baya?

A gaskiya suna da yawa amma dai na kusa-kusan nan shi ne na Kantoman Riko na Karamar Hukumar Argungu da na yi. Bayansa  kuma na zo aka ba ni mukamin Mai ba da Shawara na Musamman da sauran mukamai da dama.

Ganin yanzu kun kamala zaben shugabannin majalisa, idan kuka aiki gadan-gadan wadanne ayyuka ne kake sa ran za ka yi wa mazabarka?

To alhamdulillahi, bisa la’akari da irin abubuwan da jama’ar mazabata suke bukata, muna sa ran za mu mayar da hankali a kan gina hanyoyin karkara da samar da ruwan sha ga kauyuka ba ma kamar a Karamar Hukumar Augi. Saboda a  yankunan kauyukan Augi suna da matsalar ruwa saboda a suna da zurfin ruwa ga dutse a karkashin kasa wanda haka yana sanya shan wahala wajen gina rijiyoyi. Domin ko ’yan kwangila ba sa son a b asu aiki a wannan yanki. Don haka idan muka samu dama aka fara ayyuka za mu kai wannan ayyuka ga jama’a.

Sannan na biyu kuma akwai abin da ya shafi birane, inda za ka ga matasa suna zaune babu ayyuka don haka akwai bangar siyasa da kuma matsalar shaye-shaye. Za ka iske mutum bai da sana’a amma kuma a haka yake zama yana tsammanin samun abin da zai kai bakinsa, sai ya zama maroki ko dan bangar siyasa. Don haka wannan yana ci mini tuwo a kwarya kuma za mu hada kai da sarakuna da shugabnnin jama’a da shugabannin matasa don ganin mun samar musu da abin da za su iya rayuwa da kansu.

Ganin matasan ne ake amfani da su wajen tada zaune-tsaye da sauran ayyukan da suke kawo rashin tsaro a kasa, ko kana da wata niyya ta gabatar da wani kudiri ga majalisa don ceto matasa daga shaye-shaye da bangar siyasa?

Eh, a gaskiya kusan duk wata doka da za ka iya tunani a gabatar da ita a gaban majalisa don ceto matasa daga wadannan munanan ayyuka kusan a ce an taba yin ta. Sai dai watakila ka ce a sake bullo mata ta wata sigar wato ta wayar da kan matasan su san cewa wadannan abubuwa da suke aikatawa dama haramtattu ne a cikin kundin tsarin mulkin kasa. Misali duk abin da yake haifar da wadannan ayyuka na banga da shaye-shaye shi ne zaman banza. To idan ka fadakar da su suka san zaman banza laifi ne a cikin dokokin kasa ka ga za su tashi su nemi na kansu.

Domin abin da yake faruwa shi ne da zarar sun fara zaman banza sai kuma a koma shaye-shaye daga nan kuma wadanda suka yi sa’a sai kawai su koma maroka su rika bin mutane a wuraren suna da biki kai har ma wajen zaman makoki suna yi musu bambadanci. Wadanda kuma ba su yi sa’a ba daga cikinsu sai su koma masu aikata laifuffuka kama daga sane da sauran laifuffuka tunda yake suna shiga mutane sun saba suna ganin aljihunan jama’a a cike suna harkokin gabansu.

Don haka a halin yanzu ma abin da na yi a mazabata ta Arugungu da Augi na kafa wani kwamiti na matasa mai suna Majalisar Matasan Arugungun da Augi (Argungu/Augi Youth Parliament) wadda ita ce za ta rika  kulawa da duk wani abu da matasan yankin suke aiwatarwa. Kwamitin guda biyu ne akwai wanda za mu kaddamar a nan gaba kadan wanda zai rika zakulo mana irin wadannan matasan da suka addabi jama’a mu kuma za mu san ta yadda za mu taimaka wa rayuwarsu don ceto su daga wannan mummunar dabi’a.  Akwai kudin da muka gada daga wadanda muka karba daga hannunsu,  wadanda da su za mu yi amfani da wajen kai irin wadannan matasa wajen da za a gyara dabi’unsu bayan mu zauna tare da iyaye da ’yan uwansu da shugabanni za mu ba su Alkur’ani su rantse, a kan sun daina yin abin da suke yi, kuma sun dauki alkawarin ba za su sake komawa cikin wannan mummunar dabi’a ba, sai mu shaida musu cewa sun addabi jama’a kuma ga abin da za mu yi a kansu. Daga karshe kuma in sun gyaru sai mu samar musu da kudin da za su kama sana’a. Sannan za mu yi amfani da masarautu wadanda dama su kansu suna kafa dokokin a tsakanin  al’umma na kawar da shaye-shaye don karfafa dokokin da suke a cikin kundin tsarin mulki.

To me zai hana ka gabatar wa majalisa wani kudiri na samar da irin wannan tsari a matakin kasa?

Ka san tun kafin in zo majalisa na san waje ne na gasa sosai, kuma akwai mutanen ko ba a majalisa ba duk inda suka ji wani ya zo da wani abu na kwarai sukan yi kokari su gabatar da shi a gaban majalisar. Don haka abin da muke kokarin yi a yanzu shi ne muna son mu ga mun fara shirin can a gida kuma idan Allah Ya sa mun cimma wata nasara sai in dauko shi in zo da shi gaban majalisa.

Wadanda muka gada suna ayyuka na tallafa wa matasa da dama, amma babu wanda ya taba irin wannan, ina alfahari cewa babu wani shiri da ya kai wannan karbuwa a halin yanzu. Don mun tattara jama’a ne kowa ya kawo tasa shawara har muka cimma wannan shiri, don haka ko da ma za a canja wa wannan shiri na Youth Parliament suna, amma dai in aka yi aiki da manufarsa ina tabbatar maka cewa zai samu nasarar hana shaye-shaye da bangar siyasa a tsakanin matasa da kuma sace-sace.

Don haka za mu yi kokari mu ga ko da a Sakkwato da Kebbi ne za mu iya kafa cibiyoyin gyara matasa ta yadda ko da ’yan majalisar da muke da su a wadannan nan yankuna ne za su rika zuba wani adadi na kudin da za a rika daukar dawainiyar gyaran matasan da kuma sama musu sana’ar da ta dace bayan gyara su.

A karshe wane kira kake da shi ga al’ummarka da sauran jama’a don cimma  nasarar ayyukan majalisa?

Da farko dai a matakin sama na ji dadin yadda na ga an gina kyakkyawar alaka a tsakanin Bangaren Zartarwa da na Majalisa. A gaskiya na yi farin ciki sosai. Wannan gada da aka gina za ta haifar wa Najeriya nasara sosai. Gwamnatin Buhari ta sha fama da rashin jituwa a tsakanin wadannan bangarori , wanda hakan ya haifar da koma baya sosai. Don haka ina kira ga wadanda suka yi takara tun daga kan kansila har zuwa Shugaban Kasa wadanda suka fadi zabe su yi koyi da Shugaba Buhari wanda ya tsaya takara sau uku yana faduwa amma bai tunzura magoya bayansa su tayar da zaune-tsaye ba, duk da yake yana da yakinin shi ne yake cin zabubbukan.  Don haka ina kira ga jama’ar mazabata su kwantar da hankulansu domin da abin da suka gani na ayyukan alheri yanzu in Allah Ya yarda za su ci gaba da ganin wadanda suka fi su.