✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan farfado da kulob din Man United a kaka mai zuwa – Solskjaer

A shekaranjiya Laraba ce Kocin Manchester United na Ingila Ole Gunnar Solskjaer ya yi alkawarin zai farfado da kulob din a kakar wasa mai zuwa. Kocin…

A shekaranjiya Laraba ce Kocin Manchester United na Ingila Ole Gunnar Solskjaer ya yi alkawarin zai farfado da kulob din a kakar wasa mai zuwa.

Kocin ya ba magoya bayan kulob din hakuri jim kadan bayan kulob din Manchester City ya doke su da ci 2-0 a  gasar Firimiya ta Ingila.

Wannan ne karo na biyu a jere da ake doke Man United a gasar inda hakan ya sa ya kasance a matsayi na 6 da maki 64 kuma ana saura wasanni uku a kammala gasar.

A jibi Lahadi ne kulob din zai hadu da na Chelsea, a wasan da wadansu ke ganin da wuya in ba a sake doke United ba.

“Ina ba magoya bayan United hakuri a duk inda suke a duniya game da rashin nasarar da muke samu.  Ina fata a kakar wasa mai zuwa za a ga canji,” inji shi.

Da yawa daga cikin magoya bayan United ba su ji dadin yadda kulob din yake tangal-tangal a kakar wasa ta bana ba.