✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan fito takarar Gwamna ko Shugaban Kasa – Gudaji Kazaure

Dan Majalisar Wakilai, da ke wakiltar mazabar Roni, Kazaure da ’Yan Kwashi, Alhaji Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana cewa yana sa ran zai fito takarara…

Dan Majalisar Wakilai, da ke wakiltar mazabar Roni, Kazaure da ’Yan Kwashi, Alhaji Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana cewa yana sa ran zai fito takarara Gwamnan Jihar Jigawa ko kuma takarar Shugaban Kasa a zaben shekarar 2023. Alhaji Gudaji Kazaure ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da Sashin HJausa na Gidan Rediyon BBC, bayan da aka tambaye shi game da halin da yake ciki bayan bai samu nasara a kokarinsa na tsayawa takarar Shugabancin Majalisar Wakilai ba.

Gudaji ya amsa cewa tun bayan da Jam’iyyar APC ta ba shi hakuri game da takarar kujerar Shugaban Majalisar Wakilai, shi ma ya hakura. “Na fid da rai, amma idan Allah Ya sa an sake dawowa, to sai inda karfina ya kare.”

Gudaji ya kara da cewa yana da burin tsayawa takarar Shugaban Kasa  ko Gwamnan Jihar Jigawa domin ya taimaka wa talaka yadda ya kamata, saboda a cewarsa taimakon da yake yi wa talaka a kujerar dan majalisa ta yi kadan.

“Idan na samu ci gaba, yadda nake so shi ne takarar Shugaban Kasa ko takarar Gwamna. Dan majalisar ma ni gani nake yi ba na iya yi wa talaka wani abu sosai. Amma can inda za a kawo kayan talakawa, to can ne nake ganin zan iya kai su inda talaka zai amfana. Duk abin da gwamnati ta kawo da muke ganin zai iya wa talaka illa, in dai muna nan za mu ce a’a. Kana gani kwanan nan da babban banki suka kafa dokar ajiyar kudi cewa idan an kai ajiyar kudi za a rika cire wani abu muka mike muka ce ba mu yarda ba,” inji shi.