✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan iya ajiye aikin koyarwa a jami’a in ci gaba da waka – Dokta Danbuzu

Dokta Auwal Sani Lawal da aka fi sani da Danbuzu malami ne a jami’a ne da ke rera waka tare da yin fim. A hirarsa…

Dokta Auwal Sani Lawal da aka fi sani da Danbuzu malami ne a jami’a ne da ke rera waka tare da yin fim. A hirarsa da Aminiya ya fadi yadda sha’awarsa ga wakokin Shata ta sanya ya fara yin waka:

 

Wane ne Danbuzu?

Sunana Dokta Auwal Sani Lawal, ni malami a Jami’ar Maitama Sule da ke Kano. Duk da an haife ni ne a garin Jos ni dan asalin garin Musawa ne a Jihar Katsina. Kuma na yi karatun firamare  da sakandare da jami’a a Kano bayan da mahaifana suka dawo nan da zama.

Kana malamin jami’a kuma Dokta kuma kana waka?

A gaskiya son da nake yi wa wakokin marigayi Mamman Shata ina ganin shi ne makasudin fara wakata. Domin ina sauraren wakokinsa sosai kuma ina da kundayensu. Don haka na rubuta wakoki da dama tun shekaru da dadewa ina kwaikwayonsa amma ban samu na buga su ba. Sai kwanan nan haka kawai ina cikin duba dalibai masu jarrabawa sai na ji kawai waka nake son in rubuta kuma in buga ta. In gajarce maka labari dai rana ba ta fadi ba sai da na rubuta wakar sannan na je na buga ta.

Sannan wani dalilin da ya sanya na fara shiga fim da yin waka shi ne nasabar abin da nake koyarwa a jami’a wato Medical Geography wanda  a cikinsa na dauki wani sashe mai suna Literary Geography wanda yake da alaka da adabi ina nazarinsa, hakan ya sanya nake bincike a kan adabi.

Yaushe ka fara shiga fim da yin waka?

Na fara shiga fim a bara, yayin da na fara waka a bana.

Zuwa yanzu fina-finai nawa ka fito kuma wakoki nawa ka yi?

To fim din da na fito na farko mai dogon zango ne mai suna Azazila, sai kuma wani fim din shi ma mai dogon zango mai suna Kaddarar Rayuwa. Haka na fito a Jinsi da kuma wani fim da aka yi da harshen Ingilishi mai suna In Search of the King. In na dawo kan wakoki kuwa na yi wakoki kamar uku ta farko ita ce Matan Arewa, sai wakar da na rubuta wa wata yarinya mai suna Bilkin Arewa sai kuma Kishin Arewa. Amma ina sa ran zan ci gaba da rubutawa da rera wakoki masu ma’ana a nan gaba insha Allah.

A matsayinka na malamin jami’a, yaya mutane da dalibai suke kallonka a matsayin mawaki kuma dan fim?

To ai wannan shi ne jami’ar, in har za ka je jami’a ka tarar da kowa ra’ayi daya gare shi, to kawai ka canja makaranta. Domin a al’ada ma jami’a waje ne da za ka hadu da mutane masu mabambantan ra’ayi. Misali ni kaina duk wanda ya san ni ya san a mafi yawan al’amura idan jama’a sun yi Gabas baki daya, to ni Yamma nake yi.

Don haka a gaskiya a dalibaina dai ba su nuna mini wani abu a kan haka. A wasu lokuta ma idan na buga waka nakan aika wa tsofaffin dalibaina da na san suna sha’awar wakokina. Amma a jama’ar gari akwai masu ganin kamar hakan bai dace da ni ba.

To sai dai a koyaushe nakan tuna musu cewa shi fa malami ko na addini ko na boko mutum ne kamar kowa yana da ra’ayi da bukatunsa. Don haka bai dace ba a ce a kullum wai ana tsammani malami ya zama ba ya shiga a cikin lamurran da suka zo wa zamaninsa.

Misali akwai lokacin da na sanya wani gutsiren waka ta fim din Jinsi a kafar sadarwa ta Instagram, duk da yake a wakar ban yi rawa ba, amma sai wani mai bina a kafar ya rubuta mini yana cewa “Yanzu sai ka ce wai kana da ilimi ko?” Da har zan ba shi amsa da na shiga shafinsa na ga kowane ne sai kawai na rabu da shi. Don ba kowa ba ne za ka tsaya bata lokacinka kana musayar yawu da shi a irin wadannan kafafe.

Ta bangaren iyalanka, ko kana samun kwarin gwiwa daga gare su?

Kwarai kuwa, ina samun cikakken goyon baya. Misali na baya-bayan nan shi ne, da na buga wata waka kuma na yi bidiyonta sai na kai wa matana suka kalla. Matata ta biyu wacce Buzuwa ce da ta gama gani sai ta kalle ni ta ce ai da a ce na yi rawa a ciki da faifan bidiyon ya fi kayatarwa.

Ta yaya kake hada aikin koyarwa a jami’a da yin fim ko waka?

Ai ka san su wadannan ayyuka biyu ba koyaushe ake yin su ba. Don haka ba sa shafar aikina na koyarwa

Ko don neman kudi kake yin wakokin?

Zuwa yanzu dai saboda nishadi da sha’awa nake yi. Amma idan kudin za su zo ta wannan hanya ba fa zan ki ba. Domin a haka nakan sanya bidiyoyin wakokin nawa a kan shafina na kafar sadarwa ta Youtube, kuma duk wanda ya kalla ina samun ’yan canji.

Wane bangare wakokin ka fi mai da hankali, siyasa ko soyayya ko ilimantarwa?

A gaskiya na fi son in yi waka a kan abubuwan da suke faruwa na yau da kullum. Ba na jin zan yi wakar soyyayya, domin ni wajena soyayya kamar mafarki ce. Sannan kuma ga shi mawakan soyayyar sun cika ko’ina.

Ko za ka bar koyarwa a jami’a a nan gaba ka koma waka da yin fim kadai?

A’a, abin da ya sanya na fadi haka shi ne cewa zan iya bari idan har na ga wakokin nawa suna kawo mini kudin da suka fi na aikin. Don na taba fada wa wani abokin aikina cewa idan fa waka za ta rika kawo min kudi kundundun, zan iya ajiye aikina koda ban kai farfesa ba. Na buga masa misali da Rarara inda na fada masa in ya buga waka daya zai iya samun albashin malamin jami’a na watanni. Don haka a yanzu dai zan hada su gaba daya.

Mene ne burinka a nan gaba kan harkar waka?

Ina son a nan gaba in samu in bude sutudiyo na zamani mai kayan aiki, wanda zan iya shiga in rera wakata a duk lokacin da na ga dama. Haka kuma zan iya hada faya-fayan bidiyon waka a ciki ko kuma in hada fim a ciki.

Yaya maganar iyali?

Ina da mata biyu da ’ya’ya hudu duk maza

Wane kalubale kake fuskanta a yanzu?

Kalubalen bai wuce na kudi ba, domin wannan sutudiyo na bukatar kudi mai yawa.

Wace shawara za ka ba matasa?

Matasa ya kamata da farko su fara gano a wane fanni basirarsu take. Idan ka gano cewa basirarka a kwallo take to ka mayar da hankalinka a kanta za ka ci nasara. Amma in har Allah Ya ba ka basirar kasuwanci ka je ka kama aikin karantarwa to kuwa kana ba kanka wahala ne kawai, za dai ka samu na abinci. Ma’ana dai duk abin da mutum yake da basira a kansa in ya dauke shi da muhimmanci zai kai ga nasara har ya taimaka wa wadansu.

Wane ne gwarzonka a mawakan zamani?

Rarara mawaki ne mai basira sosai kuma ina matukar so da sauraren wakokinsa. Ba don salonsa na zambo da cin mutuncin duk wanda ba ya tare da shi ba, to da sai in ce shi ne mawakin da na fi so a cikin mawakan zamani.