Da Dumi Dumi

‘Zan iya garkuwa da dana don in samu kudi’

Wata mata da ake zargi da yin garkuwa da mutane, main suna Fatima Muhammad, ta ce za ta iya yayin garkuwa da danta na cikinta don ta samu kudi.

A ranar Litinin da ta gabata ’yan sanda a Maiduguri fadar Jihar Borno suka gabatar da Fatima da wadansu mutane da ake sarginsu da sace dan Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Alhaji Ali Bukar Dalori. Fatima da sauran wadanda ake zargin sun sace dan Dalori mai shekara hudu ne suka yi garkuwa da shi suna neman kudin fansa, kuma lokacin da aka gabatar da su a gaban manema labarai a ranar Litinin a Maiduguri ta ce: “Na aikata laifin ne saboda ina son kudi. Ba na da-na-sani a kan laifin da na aikata kuma koda a ce dan cikina ne, zan sace shi domin kudi.”

“Na san cewa dan Shugaban Jam’iyyar APC ne; na dauke shi ne saboda ina bukatar kudin da zan wataya a wani wuri. Ta yaya zan yi da-na-sanin wani abu?” inji Fatima.

Fatima da abokan zarginta sun sace Kashim Ali Bukar Dalori mai shekaru 4 ne, inda suka yi garkuwa da shi suna neman kudin fansa har Naira miliyan 20.

Fatima wadda, ita ce kanwa uwar gami kan sace yaron ta shaida wa wakilinmu cewa “Ni na tafi makarantar su Kashim na dauko shi zuwa otel din da muke kuma mun yi ne don mu samu kudin fansa mu biya bukatunmu, amma abin bai yiwu ba har zuwa wannan lokaci da muka shiga hannu. Tun farko ni da su Shehu

ADVERTISEMENT

Musa da Mukhtar Goni da kuma Shu’aibu Bana, muka shirya yin wannan abin sai muka kama daki a otel din Albarka da ke gaba da Tashar Baga Road, sai na tafi makarantar na shiga ajinsu na nemi izini daga malamansu sai muka tafi Kano in da a can ne muka tura wa mahaifiyarsa sako a wayarta cewa idan har suna so a sako shi su kawo kudin fansa Naira miliyan 20, kuma su kai Kano.”

Ta ce, sun yi haka ne bayan kwana biyu da sace yaron, amma sai jami’an tsaro suka bi su Kano har suka gano su suka shiga hannu.

“Kuma mun yi wannan ne don muna bukatar kudi saboda ba mu da kudi, amma su ’yan siyasa suna da kudi musamman shi Shugaban APC Ali Bukar Dalori,” inji ta.

Fatima ta ce ta san Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar da dukan mutanen gidansa “Shi ya sanya ma na yi gaban kaina na tafi makarantar dan nasa na dauke shi babu ko fargaba kuma yaron ya san ni, to amma ba wai na yi haka ne ba don in cutar da shi da mutanen gidansu a’a na yi haka ne don in samu kudi shi ya sanya na hada baki da wadannan mutane da nufin idan mun samu za mu raba kudin kowa ya biya bukatarsa,” inji ta.

Fatima ta shiga makarantar Maiduguri Capital School ne inda ta yi gaba da Kashim Ali Bukar Dalori, ta hanyar nuna ta zo daukarsa daga Makaranta za ta kai shi gida. Kuma bayan kwana biyu sai suka sanar da cewa yaron yana hannunsu kuma in har ana so a same shi to sai an kai kudin fansa Naira miliyan 20.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Borno, Mista Damian Chukwu ya ce Fatima da abokan zarginta da yaron suna cikin kyakkyawan yanayi lokacin da aka kama su. Kwamishinan ya ce an kama abokan haidn bakinta biyu, Muhammed Musa da Mukhtar Ali-Shu’aibu, dukansu daga yankin Bulumkutu da ke Maiduguri, a can Kano a lokacin da za su karbi kudin fansa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya