Da Dumi Dumi

Zan iya yin wakar Shata 100 a zama daya – Aliyun Shata

Aliyun Shata
Aliyun Shata

Wani matashi mai suna Aliyu Abdulkadir Batsari mazauni cikin garin Katsina da ake yi wa lakabi da Aliyun Shata ya ce zai iya kawo wakokin Shata akalla guda 100 a zama guda ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Matashin wanda wakilin Aminiya a Katsina ya tarar yana rero wakokin Shata a lokacin da wadansu mutane suka nemi ya yi don nishadantar da su, ya ce, shi da wakokin Shata mutu-ka-raba.

Aliyu Abdulkadir Batsari wanda aka haifa a garin na Batsari a Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina ya ce sun dawo cikin garin Katsina ne bisa canjin wajen aiki, saboda mahaifinsa malaman makaranta ne. “Na yi karatun firamare a nan Kofar Kaura daga nan na wuce Kwalejin Horar da Malamai ta Katsina (KTC). Amma daga nan ban wuce gaba ba,” inji shi.

To ko yaya Aliyu ya samu kansa da wakokin Shata, sai ya ce, “Son wakokin Shata sun fara shigata ne ta sanadiyar saurarensu da nake yi a rediyo a lokacin da nake tallar kwanoni. To abin bai kara karfi ba sai lokacin da na kama sana’ar gyaran rediyo. Tun daga wancan lokaci sai ya zamo ba na sauraren waka sai tasa.” Ya ce: “Sannan wakar farko da na fara so kuma na yi kokarin haddace ta, ita ce ta dan sanda ASP Audu. Wannan waka sai da ta zamo mini tamkar wani karatu domin ko me nake yi ita ce abar rerawata. Daga nan sai wakar Mai Aska Ciroman Askin Jalingo. A haka, sai ya zamo na ci gaba da sauraren sauran da kuma rera su. Da farko na yi kokarin haddacewa, amma daga baya sai batun haddar ya tashi. Sai dai kawai in wakar ta zo in yi, domin wani lokaci sai in nemi in yi amma abin ya gagara.”

“Ban mantawa, akwai wani lokaci ina kwance cikin dare, kawai sai na ji na kama yin wakokin, wasu ma ban taba jarraba rera su ba, sai a wannan dare kawai na ji ina yin su. Misali, wakar Bawa Direba (wakar da Aminiya ta tarar yana yi). Ka ji yadda abubuwan suke tafiya,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Da aka tambaye shi  ko ana gayyatarsa wurare don ya yi wakar Shatan kamar yadda aka same shi a lokacin yana yi, sai ya ce, “Eh, an taba gayyatata a garin Safana wajen wani biki na yi wakokin. Ko ni kaina ban san yawan wadanda na rera ba a lokacin sai daga baya ake shaida mini cewa na yi waka daban-daban har 80. Sannan a kofar gidan Alhaji Surajo Mai Asharralle nan ma na yi su da yawa kuma na samu alheri. Kuma ka sani wani abin ikon Allah, ban taba dauko wata wakar Shata da ban kai ta karshe ba. A ce ko ta kakare mini ko yin tari ko gargara. Muddin na fara ta to sai na kai karshe. Sai dai kuma, sai a nemi in yi wata wakar abin ya tsaya cik saboda ba ta zo ba. An kuma taba yin taron masoya Shata a Gidan Tarihi na Katsina, ban ma san ana yi ba sai wani ya shaida min, na je kuma aka ba ni dama na fito na yi wakokin. A nan ne na samu alherin da ban taba samunsa ba ta wannan hanyar. Nan ne na hadu da Lawal babban dan Shata. Shi ma Sanusi mun san juna, domin mun hadu da shi lokacin da ya zo nan Katsina. Kuma dukkansu biyun babu wanda ya nemi ya hana ni yin wakokin, hasali ma, babu wanda bai yi mini kyauta ba ta jin dadi. Gaskiya, wakokin Shata zan iya cewa, sun zama wani sashi na jikina domin na sha yunkurin in bar yin su amma abin ya gagara.”

Aliyu mai kimanin shekara 40 a duniya, yana da mata daya da ’ya’ya 7, kuma har zuwa wannan hira da shi yana sana’ar gyaran rediyo. Sai dai ya ce, yana son komawa makaranta in da zai samu tallafin yin hakan duk da cewa ya fara tara iyali. “In kuma wata sana’ar ta samu wadda ta fi gyara zan yi ta,” inji shi.

Sai dai batun yin wakar Shata sai abin da ya yi gaba, domin shi ma yana kirkiro tasa ya yi. Kuma duk wanda ya ji muryarsa a lokacin da yake wakar zai yi zaton Shata ne sai dai dan bambanci kadan.

Hotuna daga Kannywood

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya