Da Dumi Dumi

Zan kawo karshen shigo da man fetur zuwa shekarar 2023 – Shugaban NNPC

NNPC Mele Kolo Kyari
NNPC Mele Kolo Kyari

Sabon Babban Manajan Daraktan Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), Malam Kolo Mele Kyari, ya sha alwashin kawo karshen shigo da man fetur cikin Najeriya kafin karshen shekarar 2023.

Alhaji Kolo Kyari ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin taya murnar ritaya ga tsohon Shugaban Kamfanin  NNPC  Dokta Maikanti Baru a ranar Lahadin da ta gabata bayan ya cika shekara 60 a duniya.

Sabon Shugaban ya ce zai tabbatar da matatun man fetur hudu da ake da su  a kasar nan wadanda suka hada da ta Kaduna da Fatakwal da Warri an gyara su  kuma sun dawo da aikinsu domin daina shigo da tataccen mai cikin kasar nan.

Alhaji Kyari ya ce, za su karfafa wa Kamfanin Dangote domin kammala aikin gina matatar man fetur da yake yi domin a kamalla shi cikin hanzari da kuma sake bayar da dama wajen kakkafa sababbin matatun man fetur masu zaman kansu a kasar nan.

Shugaban wanda shi ne na 19 a jerin wadanda suka shugabanci Kamfanin NNPC, ya ce, “Dole ne mu tabbatar mun daina shigowa da tataccen man fetur daga waje a matsayinmu na masu arzikin man fetir.” Kyari ya fadi haka ne jim kadan bayan ya karbi takardun kama aiki a matsayinsa na Babban Manajan Daraktan Kamfanin NNPC.

ADVERTISEMENT

“Za mu yi aiki tukuru domin ganin an gyara matatu hudu da muke da su kuma za mu bawa ’yan kasuwa dama su gina sababbin matatu  kafin wa’adin wannan gwamnati mai ci ya kare. Za mu taimaka wajen ganin Kamfanin Dangote ya kammala matatar man fetur dinsa a kan lokaci. Za mu mai da Najeriya kasa mai fitar da tataccen man fetur  zuwa shekarar 2023,” inji shi.

Sabon Babban Manajan Daraktan ya sha alwashin yin aiki tukuru shi da jami’ansa domin ganin burin da Gwamnatin Tarayya take da shi na kara yawan gangar man da ake fitar da shi zuwa ganga miliyan 3 nan da  shekarar 2023.

Da yake bayani a kan shugabanci nagari ya ce, za su yi kokarin ganin an yaki cin hanci da rashawa a Kamfanin na NNPC.

Ya ce, “Shugaban Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) shaida ne dan gane da yadda Kamfanin NNPC ya canja a cikin shekara ukun da suka wuce.”

Dangane da tsohuwar al’adar nan da aka san Kamfanin NNPC da shi ta cin hanci da rashawa, Kyari ya ce za su samar da tsarin bayyana duk wasu harkokin kamfanin a fili.

“Kamfanin NNPC zai rika yin aikinsa a  fili a dukkan harkokinsa domin bayar da dama ga kowa ya san yaya kamfanin yake gudanar da harkokinsa domin sanin muna yin aikinmu daidai ko akasin haka,” inji shi.

Ya bayyana godiyarsa ga wanda ya gada  dangane da irin kokrin da ya yi a lokacin da yake jagorancin kamfanin.

Ya ce hanyar kadai da za su saka wa tsohon Shugaban shi ne su yi aiki tukuru domin ya rika tunawa da irirn gudunmawar da ya bayar a lokacin da ya yi nasa jagorancin

Da yake jawabin godiya tsohon Shugaban na NNPC Injinya Maikanti Baru ya ce ya yi iyakacin kokarinsa domin ya dora Kamfanin NNPC  a kan hanyar ci gaba.

Ya gode wa dukkan wadanda suka taimaka masa a lokacin da yake rike da shugabancin kamfanin inda ya yi musu fatar alheri. Ya ja hankalin sabon shugaban da wadanda za su yi aiki tare shi da su dubi bangaren ci gaban ma’aikatan kamfanin  tare da taimaka wa kasa wajen samar da iskar gas da kuma habaka tace man fetur a cikin kasa.

Dokta Baru ya gode wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda damar da ya ba shi wajen ya zabo wanda zai maye gurbinsa, ya ce wannan shi ne irinsa na farko a tarihin kamfanin.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya